Hawaye, Alhini Yayin Da Dan Majalisar Jihar Kogi Ya Rasu Bayan Zabe

Hawaye, Alhini Yayin Da Dan Majalisar Jihar Kogi Ya Rasu Bayan Zabe

Majalisar jihar Kogi ta rasa daya cikin manyan mambobinta.

Mamban wanda ke wakiltar mazabar Yagba a majalisar jihar, Jimoh Omiata, ya rasu.

Dan Majalisa
Dan majalisar jihar Kogi Jimoh ya rasu. Photo credit: Femi Olugbemi
Asali: Facebook

A cewar rahoton da The Punch ta wallafa, Omiata ya rasu ne a safitar ranar Laraba, 27 ga watan Fabrairu a wani asibiti da ke Legas inda ya ke jinyar wata rashin lafiya da ba a bayyana ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karin bayani dangane da rasuwar Omiata sun bayyana

Babban sakataren watsa labarai na majalisar jihar Kogi, Femi Olugbemi, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Ya rubuta:

"Abin bakin ciki, mun rasa jajirtacce, kuma dan majalisa mai karfin fada a ji, Honarabul Musa Jimoh Omiata, ina mika sakon ta'aziyya ga iyalansa, sarakunan gargajiya da mutanen mazabar Yagba East, Allah ya jikansa da rahama."

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Wakilin PDP ya yanki jiki ya fadi a wurin kirga kuri'a wata jihar Arewa

Omiata, wanda ya fito daga garin Igbagun a karamar hukumar Yagba, dan majalisa ne wanda ya yi wa'adi biyu; kuma mutum na farko da ya taba yin tazarce daga yankinsa.

Karin bayani na nan tafe ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel