Latest
Yayin da aka shiga 10 na karshe a watan Ramadana, sarkin Musulmi ya bayyana cewa, ya kamata kowa ya koma ga Allah don yiwa Najeriya addu'o'in nasara a yanzu.
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kano, tana neman kotu ta kwace nasarar da ɗan takarar jam'iyyar NNPP, ya samu a zaɓen gwamnan jihar Kano.
Hukumar kula da walwala da jin daɗin maniyyatan Kaduna ta nemi hukumar kula da aikin Hajji a Najeriya NAHCON ta kara mata kujeru 500 domin cika bukatun mutane.
An gano wata matashiyar budurwa wacce ke tuka mota kirar Tesla tana sharbar baccinta yayin da motar ta ci gaba da tuka kanta ba tare da ta kara da wani ba.
Bayanai daga lamarin da ya faru tsakanin Peter Obi da jami’an tsaron Ingila a filin jirgin sama ya tabbatar da cewar yan Obidients ne suka ceci dan takarar LP.
Wata kotu a Abuja ta bayyana soke wasu zabukan da aka gudanar a jihar Kogi kwananan nan don zabo dan takarar gwamnan jihar a APC a zaben da ke tafe a Nuwamba.
Rahotanni sun nuna cewa jita-jita ta yi ta yawo kan batun murabus din shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu. Jam'iyyar ta fito fili ta musanta hakan.
Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun bindige sufeton dan sanda, Augustine Ukegbu, a jihar Imo bayan sun yi garkuwa da shi a lokacin da ya je hutu.
Majalisar dokokin jihar Kano, ta amince da bukatar gwamna Ganduje na tabbatar da an yi gyara a kudurin masarautun jihar da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Masu zafi
Samu kari