Jam'iyyar APC Ta Garzaya Kotu, Tana Neman Kotu Ta Kwace Nasarar Abba Gida-Gida

Jam'iyyar APC Ta Garzaya Kotu, Tana Neman Kotu Ta Kwace Nasarar Abba Gida-Gida

  • Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kano ta garzaya kotu domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen gwamnan jihar
  • Jam'iyyar APC na neman kotun sauraren ƙarar zaɓen gwamnan jihar ta ƙwace nasarar Abba Gida-Gida a zaɓen
  • APC ta lissafo dalilan da ya sanya ta ke son a kotu ta ƙwace nasarar jam'iyyar NNPP da Abba Gida-Gida

Jihar Kano - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta shigar da ƙara a gaban kotun sauraren ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kano, tana ƙalubalantar bayyana Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP matsayin wanda ya lashe zaɓen da INEC ta yi.

Daily Trust ta rahoto cewa a cikin ƙarar da APC ta shigar tana ƙalubalantar cewa Abba Kabir Yusuf wanda akafi sani da Abba Gida-Gida, bai cancanci yin takara a zaɓen ba saboda babu sunan shi cikin sunayen mambobin jam'iyyar da NNPP ta aikewa INEC.

Kara karanta wannan

Hukumar INEC Ta Bayyana Kwakkwaran Dalilin Da Ya Sanya Atiku Yayi Rashin Nasara a Hannun Tinubu

APC na neman a kwace nasarar Abba Gida-Gida
Dan takarar gwamnan jam'iyyar NNPP a Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Dailypost.com
Asali: UGC

Sai dai, ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC na jihar, Nasiru Yusuf Gawuna, bai shiga cikin masu shigar da ƙarar ba, cewar rahoton The Punch

Waɗanda ke a cikin ƙarar sun haɗa da jam'iyyar APC a matsayin mai shigar da ƙara, yayin da jam'iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf da INEC ke a matsayin waɗanda ake ƙara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jam'iyyar APC ta kuma yi zargin cewa jam'iyyar NNPP ba ta lashe zaɓen jihar da mafi yawan halastattun ƙuri'u ba, inda ta ce wasu daga cikin ƙuri'un ba halastattu bane sannan idan aka cire su, APC ta samu ƙuri'u mafi yawa a zaɓen.

Jam'iyyar ta kuma yi zargin cewa kwamishinan zaɓen hukumar INEC na jihar ya yi kuskuren bayyana Abba a matsayin wanda yayi nasara, inda ta ƙara da cewa kamata yayi ace ya bayyana zaɓen matsayin wanda bai kammalu ba.

Kara karanta wannan

Gaskiyar Magana Ta Bayyana Kan Dalilin Da Ya Sanya APC Ta Kasa Karbar Mulki a Hannun PDP a Wata Babbar Jiha

APC ta bayyana buƙatun ta

Jam'iyyar APC mai shigar da ƙarar na neman kotun da ta bayyana cewa NNPP ba ta da ɗan takara, inda ta haƙiƙance cewa babu sunan Abba Yusuf a cikin sunayen da NNPP ta turawa INEC a lokacin zaɓen.

Haka kuma yana neman kotun da ta bayyana Gawuna ko APC a matsayin waɗannda suka lashe zaɓen saboda sun samu mafiya yawan ƙuri'u idan aka cire gurɓatattun ƙuri'u daga cikin waɗanda NNPP ta samu.

Idan buƙatar farko ba ta samu ba, mai shigar da ƙarar na neman kotun ta bayyana zaɓen matsayin wanda bai kammalu ba, duba da cewa tazarar da aka ba ɗan takarar ta ba ta fi yawan ƙuri'un da aka soke ba.

Waɗanda ake ƙarar suna kwanaki 21 domin yin martani kan ƙarar da ake yi musu.

Gaskiya Ta Bayyana Dangane Da Batun Murabus Din Shugaban Jam'iyyar APC Na Ƙasa

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar APC ta yi magana kan batun jita-jitar da ke yawo cewa shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abdullahi Adamu, ya yi murabus.

Jam'iyyar ta musanta labaran da ke yawo masu cewa shugaban ya yi murabus daga kan kujerar sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel