Yanzu Yanzu: Yan Bindiga Sun Kashe Sufeton Dan Sanda Da Ke Hutu a Imo

Yanzu Yanzu: Yan Bindiga Sun Kashe Sufeton Dan Sanda Da Ke Hutu a Imo

  • Wasu tsagerun yan bindiga sun kashe Augustine Ukegbu, sufeton dan sanda yayin da yake hutu da iyalansa a Imo
  • An tattaro cewa makasan sun farmaki gidan sufeton dan sandan sannan suka yi garkuwa da shi a wata bakar Jeep kirar Lexus
  • An tsinci gawarsa daga baya a jeji inda makasan suka yasar da shi tare da motar da suka dauke su a ciki

Imo - Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani sufeton dan sanda mai suna Augustine Ukegbu a jihar Imo.

An kashe babban jami'in dan sandan ne a lokacin da ya je kauyensa da ke Umuoshike Ogbor a karamar hukumar Aboh Mbaise ta jihar Imo, jaridar Punch ta rahoto.

Jami'an yan sanda rike da bindigogi
Yanzu Yanzu: Yan Bindiga Sun Kashe Sufeton Dan Sanda Da Ke Hutu a Imo Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Yadda yan bindiga suka kashe sufeton dan sanda a Imo

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Gobara Ta Tashi Ana Tsaka Da Shagalin Bikin Aure, Jama'a Sun Ci Na Kare

Jaridar The Cable ta rahoto cewa wasu majiyoyi sun ce marigayin ya je gida ne tare da iyalinsa don bikin Easter.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daya daga cikin majiyoyin sun bayyana cewa an yi garkuwa da jami'in tsaron jim kadan bayan isowarsa daga matsuguninsa a Owerri, babban birnin jihar Imo sannan daga baya aka tsinci gawarsa a wani jejri da ke kusa da Mbutu da ke karamar hukumar Aboh Mbaise.

An tattaro cewa an yi garkuwa da Sufeton da ke aiki a hedkwatar yan sandan Orji da ke jihar Imo a gidansa da misalin 11:00 na daren ranar 8 ga watan Afrilu.

Daya daga cikin majiyoyin sun ce:

"An kai rahoton sace shin ofishin yan sanda a Oke Ovoro. Daga bisani aka samu Jeep din da aka sace shi da ita a yashe a hanyar Mbutu da ke Aboh Mbaise. Jami'an yan sanda sun ziyarci wajen sannan suka binciki jeji da ke wajen, sannan aka tsinci gawar sufeton."

Kara karanta wannan

An samu tangarda: Saurayi ya fusata, ya kone gidan su tsohuwar budurwarsa kurmus

Majiyar ta kara da cewar wasu jami'an yan sanda sun ajiye gawar sufeton dan sandan a dakin ajiye gawa yayin da aka samo motar da aka sace shi a ciki.

Zababben dan majalisar Borno mai wakiltan mazabar Chibok ya kwanta dama

A wani labarin kuma, mun ji cewa Allah ya amshi ran zababben dan majalisar dokokin jihar Borno mai wakiltan mazabar Chibok, Clark Nuhu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel