Kotu Ta Rushe Sabon Kwamitin Shugabannin PDP Na Riƙo a Jihar Katsina

Kotu Ta Rushe Sabon Kwamitin Shugabannin PDP Na Riƙo a Jihar Katsina

  • Babbar Kotu ta kara dagulawa jam'iyyar PDP lissafi a jihar Katsina bayan kammala babban zaɓen 2023
  • Alkalin Alkalan jihar Katsina ya rsuhe kwamitin rikon kwarya da PDP ta kafa a Katsina bayan tsige shugabanni
  • Ya umarci INEC karta aminta da wani shugaba daga cikin kwamitin har sai Kotu ta gama sauraron ƙarar da aka shigar gabanta

Katsina - Babbar Kotun jihar Katsina, ranar Talata, ta rushe sabon kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar PDP da aka kafa a jihar da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Idan baku manta ba kwamitin gudanarwan PDP ta ƙasa (NWC) ya naɗa kwamitin rikon kwarya bayan amincewa da tsige baki ɗaya shugabannin jam'iyya na Katsina ranar 23 ga watan Maris.

Tutar PDP.
Kotu Ta Rushe Sabon Kwamitin Shugabannin PDP Na Riƙo a Jihar Katsina Hoto: PDP
Asali: Twitter

Kotun ta yanke wannan hukuncin na korar kwamitim rikon kwaryan da PDP ta naɗa a ƙarar da tsohon shugaban jam'iyyar, Salisu Uli, da wasu mutum 9 suka shigar gabanta.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Shugaban 3SC Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Shugaban Alƙalan jihar Katsina, Mai shari'a M. D. Abubakar, wanda ya jagoranci shari'ar, shi ne ya yanke hukuncin cikin shari'a kan batun, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya umarci wanda ake kara na farko, Abdulrahman Usman, (da sauran mambobin kwamitin riƙon) su dakata daga tafiyar da harkokin PDP reshen Katsina har sai Kotu ta yanke hukuncin ƙarshe.

Bayan haka Kotun ta umarci wanda ake kara na 2 da na uku watau PDP da INEC, karsu aminta da ko ɗaya daga cikin mambobin kwamitin rikon su ja ragamar PDP reshen Katsina.

A ruwayar Dailypost, Alkalin ya ce:

"Masu kara su tabbata sun sanar da waɗanda ake tuhuma kafin zama na gaba ranar 15 ga watan Mayu, 2023, idan suka gaza kuma umarnin ya rushe."

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa jihar Katsina na ɗaya daga cikin jihohin da jam'iyyar PDP take fama da rikicin cikin gida tsakanin tsohon gwamna, Ibrahim Shema da Sanata Yakubu Lado.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Fitattun Sanatocin Arewa 5 Da Ke Neman Zama Shugaban Majalisar Dattawa

Wani mamban PDP da ya wakilce ta lokacin zaɓe a karamar hukumar Ɗanja, jihar Katsina, Kabir Abdullahi, ya shaida wa Legit.ng Hausa cewa rigingimun cikin gida ne suka kawo musu cikas.

Jigon ya ce matsalar da ta shiga tsakanin manyan PDP a Katsina ce ta jawo musu rashin nasara a babban zaɓen 2023 da aka kammala.

Da yake zantawa da wakilinmu, Abdullahi ya ce:

"A zahirin gaskiya na fi yarda da tsagin ɗan takarar gwamnan mu, Yakubu Lado, amma wannan rikicin na PDP ya zarce tunanin mu, ga shi har yanzun bai kare ba, magana na gaban Kotu."
"Na yi tsammanin za'a zo nan, sai dai duk da haka muna nan daram a PDP, amma ya zama wajibi shugabanni su sasanta kansu, domin sulhu alkairi ne, matuƙar ba sulhu aka yi ba, to ban hangi karshen rikicin nan ba."

APC ta canja tsarin fidda ɗan takarar gwamna a jihar Kogi

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar PDP Ta Sanar da Sakamakon Zaben Fidda Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Bayelsa

A wani labarin kuma APC Ta Yi Amai Ta Lashe, Ta Amince da Tsarin Kato Bayan Ƙato a Zaben Fidda Gwani a Jihar Kogi

A wata wasiƙa da ta aike wa INEC, Jam'iyya mai mulki ta ce zata bi tsarin kato bayan kato wajen fidda ɗan takarar gwamna maimakon tsarin Deleget.

Asali: Legit.ng

Online view pixel