Sakataren Jam'iyyar PDP Na Kasa Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin Gwamnan Jihar Imo

Sakataren Jam'iyyar PDP Na Kasa Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin Gwamnan Jihar Imo

  • Sakataren jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na ƙasa, Samuel Anyanwu ya lashe zaɓen fidda gwanin gwamnan jihar Imo
  • Sanata Samuel Anyanwu zai yi takarar gwamnan jihar inda zai fafata da gwamnan APC mai ci, Hope Uzodinma
  • Jam'iyyar PDP na ƙokarin sa ke amsar ragamar mulkin jihar Imo a hannun jam'iyyar APC mai mulki

Jihar Imo - Sanata Samuel Anyanwu, sakataren jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na ƙasa, ya lashe zaɓen fidda gwanin ɗan takarar gwamnan PDP a jihar Imo.

Za a gudanar da zaɓen gwamnan jihar ne dai a ranar 11 ga watan Nuwamban 2023.

Samuel Anyanwu ya lashe zaben fidda gwanin gwamnan PDP a Imo
Sakataren jam'iyyar PDP na kasa, Sanata Samuel Anyanwu Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Nasarar Sanata Anyanwu ta samu ne biyo bayan zaɓen fidda gwanin gwamnan PDP na jihar wanda aka gudanar ranar Laraba a sakatariyar jam'iyyar da ke akan hanyar Okigwe, cikin Owerri babban birnin jihar Imo, rahoton Channels Tv ya tabbatar

Kara karanta wannan

Kato Bayan Ƙato: Jam'iyyar APC Ta Yi Amai Ya Lashe, Ta Sauya Tsarin Gudanar Zabe A Jihar Arewa

Za a gudanar da zaɓukan gwanoni wanda ba na gama-gari a jihohin Bayelsa, Kogi da Imo a ranar 11 ga watan Nuwamban 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar sakataren tsare-tsaren jam'iyyar PDP na jihar Imo, Lawrence Biado, kwamitin mutum bakwai da kwamitin gudanarwa na ƙasa na PDP ya kafa domin sanya ido akan zaɓen, yana wajen domin sa ido kan yadda zaɓen ya gudana a jihar.

The Pledge ta rahoto cewa, tsohon gwamnan jihar, Emeka Ihedioha, bai halarci wajen zaɓen fidda gwanin ba. A kwanakin baya ne dai Ihedioha ya janyw daga takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP.

Ihedioha ya janye daga takarar ne a lokacin bayan ya yi zargin cewa ba za ayi adalci ba a zaɓen fidda gwanin gwamnan na jam'iyyar PDP a jihar.

Anyanwu zai fafata da gwamnan jihar mai ci yanzu Hope Uzodinma, wanda yake neman tazarce a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Kogi: Jerin Manyan Yan Siyasar PDP 5 Da Ke Son Karbar Mulki Daga Hannun Yahaya Bello

A watan Janairun 2020, kotun ƙoli ta tsige Ihedioha a matsayin gwamnma jihar Imo, bayan ya yi wata bakwai kacal akan mulki.

Jam'iyyar APC Ta Garzaya Kotu, Tana Neman Kotu Ta Kwace Nasarar Abba Gida-Gida

A wani labarin na daban kuma, kun ji yadda jam'iyyar APC a jihar Kano ta garzaya kotu tana neman a ƙwace nasarar Abba Gida-Gida.

Jam'iyyar ta ce ɗan takarar na NNPP bai cancanci lashe zaɓen gwamnan na jihar Kano ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel