Wike Zai Lalata Kulle-Kullen da PDP, LP da NNNP Suke Yi wa APC a Zaben Shugaban Majalisa

Wike Zai Lalata Kulle-Kullen da PDP, LP da NNNP Suke Yi wa APC a Zaben Shugaban Majalisa

  • Nyesom Wike ba zai yarda jam’iyyar PDP ta birkitawa APC lissafi a takarar shugaban majalisa ba
  • Gwamnan jiha Ribas ya ce masu rinjaye ne suke da hakkin fito da wadanda za su zama shugabanni
  • Wike ya sanar da ‘ya ‘yan jam’iyyarsa cewa ‘yan majalisan jihar Ribas ba su tare da sauran ‘yan adawa

Abuja - Gwamna Nyesom Wike bai goyon bayan yunkurin da jam’iyyar hamayya ta PDP take yi na daura mutanenta a matsayin shugabannin majalisa.

Duk da yana ‘dan jam’iyyar PDP, The Nation ta ce Nyesom Wike yana adawa da shirin da ake yi na yakar APC a zaben shugabannin 'yan majalisar tarayya.

Da ‘yan jarida suka zanta da Mai girma Gwamnan a garin Fatakwal, ya nuna shirin da jam’iyyarsa take yi ba abin da zai kawo masu zaman lafiya ba ne.

Kara karanta wannan

Allura Ta Tono Garma: APC Ta Kawowa Kotu Hujjar da Za Ta Iya Ruguza Takarar Peter Obi

Gwamna Wike ya shaidawa manema labarai ‘yan majalisan Ribas ba za su goyi baya ba.

Ana kamun kafa da Wike

A cewar Gwamnan na Ribas, duk da bai cikin ‘yan jam’iyyar APC, manyan ‘ya ‘yanta da ke neman shugabancin majalisa sun nemi ya mara masu baya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Akwai ‘yan takaran kujerar shugaban majalisar wakilan tarayya da na majalisar dattawa da suka nemi goyon bayan Gwamnan ido da ido ko ta salula.

Nyesom Wike
Gwamna Nyesom Wike Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Mutane sun zo sun gana da ni. Hon. Wase (Hon. Ahmed Idris) ya zo. Sanata Godswill Akpabio ya zo. Gwamna David Umahi ya zo.
Uzor Kalu ya kira ni sau da yawa ta wayar salula daga Amurka. Me nake fada? Ba na jam’iyyarsu, damukaradiyya maganar rinjaye ce.

- Nyesom Wike

Rahoton ya kara da cewa Gwamnan ya ce ya ji ‘yan jam’iyyaradawa su na taro domin shugabancin majalisa ya fada hannunsu, ya ce ba zai yarda da wannan ba.

Kara karanta wannan

Gwamnoni Sun Hango Matsala a Majalisa, Sun Nemi a Dauki Matakin Gaggawa a APC

Wike ya bukaci ‘yan adawa da ke majalisar tarayya da su kyale jagororin jam’iyyar APC su zabi wadanda za su zama shugabanni domin wannan hakkin su ne.

Abin da Gwamnan mai barin mulki yake so shi ne APC tayi la’akari da sarkakiyar Najeriya wajen zakulo wadanda za su shugabanci majalisun tarayyar kasar.

Obi, LP v APC

Rahoto ya zo cewa Lauyan APC a kotun zabe, Thomas Ojo zai jikawa Peter Obi aiki bayan LP ta shigar da karar zaben shugaban Najeriya da aka yi a Fubrairu.

Kamar yadda Lauyan yake fada, tun farko tsohon Gwamnan na jihar Anambra ba 'Dan LP ba ne. Jam’iyya mai-ci ta na zargin Obi da saba dokar zabe na kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel