Ganduje Ya Mika Bukatu da Yawa Gaban Majalisa, an Amince Masa da Batun Masarautun Kano

Ganduje Ya Mika Bukatu da Yawa Gaban Majalisa, an Amince Masa da Batun Masarautun Kano

  • Yana da dab da sauka, gwamna Ganduje ya bayyana wasu sabbin kudurori tare da mika su ga majalisar dokokin jihar
  • Ya zuwa yanzu, ya mika bukatu a cikin wata wasikad a suka kai akalla biyar don neman amincewar majalisar jihar
  • A ranar 29 ga watan Mayun bana ne Ganduje zai sauka a mulki, zai mika wa Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP

Jihar Kano - Kudurin gyara masarautun jihar Kano na 2019 ya shiga dokar jihar yayin zaman majalisar dokoki na gaba, rahoton Aminiya.

Wannan na fitowa ne daga bakin babban sakataren majalisar, Uba Abdullahi, inda ya bayyana cewa, an amince da kudurin ne a babban zauren majalisar.

Hakazalika, ya ce majalisar ta samo sako daga gwamna Abdullahi Umar Ganduje na neman a tabbatar da Mahmoud Balarabe a matsayin shugaban hukumar korafe-korafe da yaki da rashawa a jihar.

Kara karanta wannan

Lambar Ministoci 2 Ya Fito da ‘Yan Majalisa Ke Binciken Satar Gangunan Mai Miliyan 48

Gwamna Ganduje ya samu gata a majalisar Kano
Jihar Kano da ke Arewa maso Yamma | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Batun ya tafi gaban kwamitin yaki da rashawa

A cewar sakataren, tuni majalisa ta Kano ta mika batun zuwa kwamitinta na yaki da rashawa domin duba da kuma nazari a kai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A bangare guda, gwamna Ganduje ya mika wata bukatar a kudin da ke neman kafa hukumar kula da hanyoyin karkara.

Wannan ma haka, majalisa ta mika shi ga kwamitin da ya dace domin duba da kuma tantance manufa don amfanar al’umma.

Batun taken jihar Kano

A daya bangare kuma, gwamna Ganduje ya ce, majalisar ta yi duba ga bukatar fara amfani da taken jihar da jami’ar Bayero da gwamnatinsa suka tsara.

Hakazalika, ya turo wata wasikar da ke bayani game da dokar mallakar fili a jihar domin duba da amincewar majalisar, rahoton Naija News.

Daga karshe, Ganduje ya nemi majalisar ta tabbatar da Balarabe Hassan Karaye a matsayin sabon shugaban hukumar zabe ta jihar. Kana, ya gabatar da batun da ya shafi inshoran lafiya.

Kara karanta wannan

Jagaba Ba Za Ka Shiga Villa Ba: Kotu Ta Hana Belin Mai Zanga-Zangar Kin Jinin Rantsar Da Tinubu

Duk wanda ke gini a filin gwamnati ya dakata, inji Abba Gida-Gida

A wani labarin, kun ji yadda zababben gwamnan jihar Kano ya mika sakon gargadi ga dukkan wadanda ke gini a filin da aka ce na gwamnati ne.

Sabon gwamnan ya fadi hakan ne jim kadan bayan da aka ba shi takardar lashe zabe daga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).

Ana ci gaba da kai ruwa rana kan batun da ya shafi filaye da kuma gine-gine a jihar ta Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel