Mace Ta Fito Takarar Shugabancin Majalisa, Ita Kadai Za Ta Gwabza da Maza Kusan 10

Mace Ta Fito Takarar Shugabancin Majalisa, Ita Kadai Za Ta Gwabza da Maza Kusan 10

  • Miriam Onuhoa (APC-Imo) ta ayyana shirinta na neman takarar kujerar shugabancin majalisa
  • ‘Yar majalisar ta ce maza sun rike madafan iko, ba a damawa da ‘yanuwanta mata sosai a siyasa
  • Onuhoa tana ganin shugabancinta zai taimakawa ‘yanuwanta mata da kuma matasa a Najeriya

Abuja - Miriam Onuhoa (APC-Imo) ta ayyanawa Duniya shirinta na neman zama shugabar majalisar wakilan tarayya a majalisa ta goma.

Tribune ta ce Honarabul ta bayyana cewa akwai bukatar a sa dokar-ta-baci a kan yadda ake hana mata samun kujeru na shugabanci a kasar nan.

‘Yar majalisar ta ce a siyasar Najeriya, maza sun yi ba-ba-ke-re, sun hana mata samun shugabanci, wannan shi ne abin da take neman yaka.

Bayanin Miriam Onuhoa ya fito ne a yau Laraba a garin Abuja lokacin da ta sanar da kowa cewa ta na neman zama shugaban majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

Gwamna Gandije ya caba, majalisa ta amince da kudurinsa kan masarautun Kano

Maza za su janyewa Miriam Onuhoa

Rahoton ya ce Onuhoa ta bukacin mazan da ke da buri irin na ta su janye mata saboda a samu daidaito a kason mukamai tsakanin su da maza.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Idan tayi nasarar samun shugabanci a majalisar kasar, ‘yar siyasar ta dauki alwashin tafiya da kowa tare da kuma sanadiyyar bunkasa tattalin arziki.

Majalisa
Miriam Onuhoa a Majalisa Hoto:thewhistler.ng
Asali: UGC

Daga cikin alkawarin da Hon. Onuhoa ta dauka shi ne za ta kawo wakilci na gari a majalisa, ta ce za ta zama shugaba mai duba matsalar mutane.

A karkashin jagorancinta, Vanguard ta rahoto ‘yar siyasar tana mai cewa za a bude kofar aiki da masu ruwa da tsaki wajen yi wa Najeriya dokoki.

Tsuntsu biyu da tarko daya

Zamanta shugabar majalisa zai taimaka wajen jifar tsuntsu biyu da tarko daya, daga ciki shi ne an samu daidaito tsakanin mata da maza a majalisa.

Kara karanta wannan

Gwamnoni Sun Hango Matsala a Majalisa, Sun Nemi a Dauki Matakin Gaggawa a APC

Zaben mace a matsayin shugabar majalisa zai sa a rika damawa da matasa, sannan ta ce za ta tabbatar an maida hankali wajen amfani da fasaha.

Takarar 2023 za ta dauki zafi

Hakan ya na nufin za ta tunkari Hon. Ahmed Wase; Hon. Muktar Aliyu Betara, da Hon. Yusuf Gagdi da aka samu rahoto cewa su na neman takarar.

Akwai masu neman kujerar da ba su kai ga ayyanawa ba, su ne: Hon. Tajudeen Abbas. Hon. Aminu Sani Jaji; Sada Soli sai Hon. Makki Yalleman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel