Latest
Bayan rantsar da sabon gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bada umurnin korar dukkan wadanda tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya nada mukami a Kano.
Da safiyar ranar Talata ne jami'an tsaro na farin kaya wato DSS, suka mamaye ofishin hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), da ke Ikoyi jihar Legas.
Mun tattaro abubuwan Bola Tinubu ya fada a wajen rantsar da shi. Shugaban ya kawo maganar tallafin fetur, ayyukan yi, tsaro, ya dage sosai a kan sha’anin matasa
Kamfanin Mai ta Najeriya (NNPC) ya goyi bayan cire tallafin mai da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi lokacin bikin rantsar da shi a ranar Litinin 29 ga watan Mayu
Sabon gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, watau Abba Gida-Gida ya kori shugaban hukumar jin dadin alhazai da sauran mambobin majalisar gudanarwa baki ɗaya.
Daniel Bwala, hadimin dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, ya taya shugaban kasa Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima murnar kama aiki.
Dr. Dikko Umaru Radda ya fitar da mukaman farko. Arch. Ahmed Musa Dangiwa ya zama SSG, Jabiru Tsauri da Barr. Muhtar Aliyu Saulawa sun zama shugabannin fadar
Sabon gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf(wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ya sha alwashin sake bude shari’ar kisan kai da ake yi wa Alhassan Ado Doguwa.
Kafin Muhammadu Buhari ya bar ofis, ya nada sababbin Darektoci a tashar talabijin na NTA. A yayin da aka sanar da nadin, Bola Tinubu ya karbi mulkin Najeriya.
Masu zafi
Samu kari