Kada Ku Damu: NNPC Ya Tura Sako Ga ’Yan Najeriya Bayan Tinubu Ya Cire Tallafin Man Fetur

Kada Ku Damu: NNPC Ya Tura Sako Ga ’Yan Najeriya Bayan Tinubu Ya Cire Tallafin Man Fetur

  • Shugaban kamfanin NNPC ya ce matakin da Bola Tinubu ya dauka na cire tallafin mai ya yi dai-dai kuma suna goyon baya
  • Kyari ya bayyana haka ne a wani taron gaggawa don mai da martani akan cire tallafin da Shugaba Tinubu ya yi a bikin rantsarwa
  • Mele Kyari ya ba da tabbacin kamfanin na da wadataccen mai da zai biya bukatun ‘yan Najeriya har na tsawon wata daya a kasar

FCT, Abuja Kamfanin Mai ta Najeriya (NNPC) ya goyi bayan cire tallafin mai da Shugaba Bola Tinubu ya yi lokacin da ya ke jawabi a bikin rantsar da shi a ranar Litinin 29 ga watan Mayu.

Tinubu ya bayyana cire tallafin ne a bikin rantsar da shi inda ya ce ya cire ne saboda kasafin kudin shekarar 2023 bai ba da gurbin tallafin mai ba.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya su Shirya, NNPC Ya Kara Farashin Man Fetur a Duk Gidajen Mai da Ke Karkashinsa

Mele Kyari
Shugaban Kamfanin NNPC ya Goyi Bayan Cire Tallafi, Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Da yake jawabi a taron gaggawa a Abuja, shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari ya ce cire tallafin an yi shi ne saboda ci gaban kamfanin, cewar gidan talabijin na Channels.

Kyari ya kara da cewa kamfanin ya na kashe makudan kudade daga cikin ribar da suke samu don biyan kudin tallafin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kyari ya ce suna da isasshen mai da zai wadaci 'yan Najeriya

Ya kara da cewa bai kamata mutane su tsorata su fara layi a gidajen mai ba don siyan mai da yawa saboda su boye, cewar Punch.

Ya ce suna da wadataccen mai a kamfaninsu da zai wadaci ‘yan Najeriya har na tsawon wata daya, yayin da yace suna kula da samarwa da kuma rarraba mai din a fadin kasar.

Kamfanin ta goyi bayan cire tallafin

Mele Kyari ya tabbatar da goyon bayansa akan matakin da Shugaba Bola Tinubu ya dauka akan cire tallafin yayin da ya tabbatar wa ‘yan Najeriya wadatuwar mai din a fadin kasar ganin yadda aka fara layi a gidajen mai.

Kara karanta wannan

"Tallafin Man Fetur Ya Tafi," Shugaba Tinubu Ya Fara Ɗaukar Matakai Masu Tsauri

Ba sabon abu bane a ga 'yan Najeriya sun cika gidajen mai domin sayen mai a bangarori daban-daban na kasar.

NNPC Ta Ci Gaba Da Aikin Tonon Mai a Borno Bayan Tsawon Lokaci da Dakatarwa

A wani labarin, kamfanin mai ta NNPC ya ci gaba da aikin tono da kuma binciken mai a wasu yankuna a jihar Borno.

Kamfanin ya bayyana dalilan da yasa suka tsaida hakar mai din tun shekarar 2017 da cewa rashin tsaro shi ne babban dalili.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel