Magidanci Ya Ɗauki Budurwarsa Sun Je 'Hotel', Ya Ci Karo Da Matarsa Tare da Wani

Magidanci Ya Ɗauki Budurwarsa Sun Je 'Hotel', Ya Ci Karo Da Matarsa Tare da Wani

  • Wani magidanci da ya ɗauki abokiyar sharholiyarsa zuwa Otal domin su ji daɗinsu, ya ga abinda bai taɓa tsammani ba
  • Mutumin ya ga matarsa, wacce a tsammaninsa tana gida, ta zo Otal ɗin tare da wani na daban
  • Wannan labari ya haddasa cece-kuce a shafukan sada zumunta kuma mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu

Wani mutumi da ya ɗauki 'yar magajiya zuwa Otal domin sharholiyarsu kamar yadda suka saba ya ci garo da matarsa ta aure wacce ya baro a gida tare da nata saurayin.

Wani lauya @Bolanlecole ne ya wallafa labarin yadda lamarin ya faru a shafinsa na dandalin sada zumunta Tuwita.

Otal.
Magidanci Ya Ɗauki Budurwarsa Sun Je 'Hotel', Ya Ci Karo Da Matarsa Tare da Wani Hoto: Alistair Berg da Andersen Ross. Mun yi amfani da Hoton domin misali
Asali: Getty Images

Magidancin ya garzaya Otal ɗin tare da budurwarsa domin holewa amma sai lamarin ya juye, sai ga matarsa da na ta abokin cin amanar.

Bayanai sun nuna mutumi ya nemi Otal mafi nisa da gidansa na aure domin ya hole da yarinyarsa amma duk da haka ya yi ido hudu da mai ɗakinsa a can.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda miji ta mata suka haɗu a Otal

Lauyan ya bayyana cewa mijin ya gama fitowa tsaf lokacin da ya yi karo da matarsa, kuma dukkansu sun ga juna babu wanda zai iya wayancewa ko ya yi fuska.

Wani bangaren labarin ya ce:

"Wai meke faruwa da al'ummarmu ne, cin amana ya zama ruwan dare a zamanin nan."
Wani abokina lauya ya bani labari yanzun nan cewa wani mutumi ya ja budurwarsa Otal mai nisa don su ji daɗi, kawai ya yi kiciɓus da matarsa tare da wani suna fitowa daga wannan Otal ɗin. Sun ga junansu."

Kaɗan daga martanin mutane kan lamarin

@Teflon_phantom ya ce:

"Wannan ba sabon abu bane a yanzu, ya saba faruwa tun kafin wannan lokacin"

@Ekejo ya rubuta cewa:

"A jihar Legas musamman a Anguwar Lekki Phase 1, Ma'aurata na gayyatar wasu daban har gida domin aikata cin amana."

@BeansCFR ya ce:

"Idan nine mutumin nan, zan rabu da budurwata ne na rungume matata."

Sabon Bincike Ya Nuna Lokacin Da Ya Fi Dacewa Namiji Ya Kwanta Da Matarsa Su Raya Sunnah

A wani labarin kuma Kwararrun masu bincike a Burtaniya sun gano lokacin da ya cancanta mata da miji su yi kwanciyar aure.

A cewar binciken, amfani da irin wannan lokacin yana kara dankon soyayya da farin ciki mai ɗorewa tsakanin masoyan biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel