Abba Gida Gida Ya Kori Dukkan Wadanda Ganduje Ya Nada Mukami, Ya Umurci A Kwato Kadarorin Da Ya Sayar

Abba Gida Gida Ya Kori Dukkan Wadanda Ganduje Ya Nada Mukami, Ya Umurci A Kwato Kadarorin Da Ya Sayar

  • Sabon gwamnan Kano da aka rantsar, Abba Gida Gida ya sake daukan wani mataki kan gwamnatin magabacinsa, Abdullahi Ganduje, cikin awa 24 bayan kama aiki
  • Abba Gida Gida ya sallami dukkan masu rike da mukaman siyasa da ke jagorantar hukumomin gwamnati da kamfanoni nan take
  • A wani rahoton, gwamnan ya kuma ce zai bada umurnin a binciki batun bashi da gwamnatin ta Ganduje ta bari a jihar

Jihar Kano - Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf (da aka fi sani da Abba Gida Gida) ya sallami wasu daga cikin jami'an gwamnatin tsohon Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

A cikin wata takarda da ya saka wa hannu, sabon gwamnan ya bada umurnin cewa 'an sallami dukkan masu shugabancin hukumomin gwamnati da kamfanoni nan take,' Daily Trust ta rahoto.

Abba Gida Gida na cigaba da waiwayar ayyukan gwamnatin Ganduje
Abba Gida Gida ya sake daukar wani mataki na bincikar ayyukan gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje na Kano. Hoto: Abdullahi Ganduje
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma soke dukkan kwamitocin amintattu na hukumomin gwamnati, kamfanoni da manyan makarantun gaba da sakandare a jihar ta Kano.

Gwamnan ya kuma umurci jami'an tsaro ciki har da Hisbah nan take su mamaye dukkan kadarorin gwamnati da tsohuwar gwamnatin magabacinsa ta sayar har sai gwamnatinsa ta yi bincike ta dauki mataki na karshe.

Kalamansa:

"A yau, ina sanar da cewa jami'an tsaro karkashin jagorancin yan sanda, DSS, Civil Defense da Hisbah su karbe dukkan filayen gwamnati da kadarori da gwamnatin Ganduje ta sayar ba bisa ka'ida ba har sai gwamnati ta dauki mataki na karshe."

Abin da ke faruwa a baya-bayan nan dangane da Abba Gida-Gida, APC, NNPP, Abdullahi Ganduje, Zaben 2023

Gwamnan ya kara bayani cewa kadarorin da ya ke magana sun hada da makabartu da filayen tsaftace iska, filayen makarantu, filayen da ke kusa da ganuwa, wuraren addini da al'adu da asibitoci.

Ya kara da cewa an sayarwa na hannun daman tsohon gwamnan filaye a jihar da wajen jihar Kano.

Abba Gida Gida Ya Yi Alkawarin Bincikar Bashin Biliyan 241 Da Gwamnatin Ganduje Ta Bari A Kano

A wani rahoton kun ji cewa sabon gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da aka yi wa lakaci da Abba Gida Gida ya ce zai binciki bashin naira biliyan 241 da ya gada daga gwamnatin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Abba Gida Gida ya kuma yi korafi cewa takardun mika mulki da tsohon gwamna Ganduje ya mika masa ta hannun Sakataren Gwamnatin jiha mai barin gado sun yi kadan, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel