Latest
Nasir El-Rufai ya tsokano rikici a APC da ya bada sunan wanda yake so ya maye gurbinsa a Ministoci, wasu sun ce bai dace El-Rufai ya tsaida wanda yake so ba.
Babban Bankin Najeriya, CBN ya bayyana masu amfani da karfinsu don karya darajar Naira tare da daga darajar Dala don biyan bukatar kansu, ya saka musu takunkumi
A wani bidiyo da ya yadu, Lola Ade-John, sabuwar ministar yawon bude ido ta sanya hannu a takardar kama aiki sannan ta duka ta gaishe da shugaba Bola Tinubu.
Sabon ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya tada hankalin jama’a da ya fadi manufofinsa, zai fatataki ‘yan kasuwa da masu acaba da keke napep.
Shugaba Tinubu ya bukaci ministocinsa 45 da su yi wa kasar aiki cikin mutunci sannan su aiwatar da ayyukan da aka ba su ba wai ga jihohi ko yankunansu kadai ba.
Har yanzu ba a shawo kan rikicin PDP da gwamnonin G5 da suka yi yakin neman adalci da daidaito ba amma basu taya Wike murnar zama minista karkashin APC ba.
Sabon ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana adadin gwamnonin PDP da suka gabatarwa Shugaban kasa Bola Tinubu sunayen mutane don nada su mukamai.
Wani dan asalin jihar Kano a shekarun baya ya girgiza WAEC ta yadda sai da suka nemi ya sake rubuta jarrabawa a wani yanayi na nuna shakku kan sakamakonsa.
Ministar harkokin jin ƙai da yaye talauci, Dakta Betta Edu, ta bayyana cewa shugavan ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na shirin cire yan Najeriya daga kangin talauci.
Masu zafi
Samu kari