Wike Zai Sa Kafar Wando Daya Da Makiyaya Da ‘Yan Acaba Da Zama Ministan Abuja

Wike Zai Sa Kafar Wando Daya Da Makiyaya Da ‘Yan Acaba Da Zama Ministan Abuja

  • Sabon ministan babban birnin tarayya Abuja zai yaki wadanda yake ganin sun bata tsarin da aka yi
  • Nyesom Wike zai fatataki ‘yan kasuwa da masu acaba da keke napep da su ka cika babban birnin kasar
  • Tsohon Gwamnan zai karbe gidajen da aka gagara ginawa, ya ce hakan ya na zama barazana ga tsaro

Abuja - Jim kadan bayan rantsar da shi a matsayin ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya tada hankalin jama’a da ya fadi manufofinsa.

Da yake zantawa da jama’a da manema labarai a ma’aikatarsa, AIT ta rahoto mai girma ministan ya na bayanin yadda zai dawo da martabar birnin Abuja.

Nyesom Wike ya yi alkawari Abuja zai shiga cikin biranen da ake ji da su a duniya, amma da alama dole a kawo matakan da mutane za su koka da su.

Kara karanta wannan

"Abuja Ba Fatakwal Ba Ce": Hadimin Atiku Ya Gargadi Wike, Ya Gaya Masa Abin Da Yakamata Ya Yi

Nyesom Wike Tinubu
Bola Tinubu ya nada Nyesom Wike ya zama Ministan Abuja Hoto: @Topboychriss
Asali: Twitter
"Za mu tattauna da masu ruwa da tsaki da sauran jama’a, da masu kiwo. Dole a daina ganin shanu a Abuja, ba za mu kyale shanu na yawo cikin birni ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za su iya yin kiwonsu a wajen gari amma ba birni ba. An shuka ciyayin nan ne domin kawata birnin, ba irin ciyawar da dabbobi za su rika ci kenan ba."

- Nyesom Wike

Tashar ta rahoto tsohon gwamnan ya na cewa za su tatauna da makiyaya, domin ya na da muhimmanci a daina cin karo da tumaki a hanyar Aso Rock.

Kasuwanni sun cika Abuja - Wike

Har ila yau, sabon ministan ba zai bari kasuwanni su cika ko ina kaca-kaca ba, ya ce ba za ta yiwu ba.

"Ko ina kasuwa ne, ba za mu lamunta ba. Na san abubuwa sun yi wahala, amma bai nufin a takurawa al’umma, dole neman abinci ya zama a kan doka.

Kara karanta wannan

“Ina Dalili”: Suka, Martani Kan Nadin Hadimai Mata 131 Da Gwamnan Arewa Ya Yi

Ba za a ce mutane su na wahala, saboda haka ko ina ya zama kasuwa ba. Ba za mu yarda da wannan ba. Mutane su na saida kaya karkashin lema a birni."

- Nyesom Wike

A cewar Wike, hakan ya na jawo rashin tsaro kamar yadda ake barin kango ba a karasa ginawa ba.

Nyesom Wike zai karbe gidaje

Punch ta rahoto jigon na PDP ya na cewa zai fatattaki masu babur da keke napep, a cewarsa masu hayar na kawo cinkoso bayan jefa rayuka a hadari.

Wadanda su ka bar gidajensu su zama mafakar marasa gaskiya za mu karbe su. Ka yi shekaru 15 ka na gina gida. Kango ya zama wurin marasa gaskiya.

Gwamnati za ta karbe gidajen nan musamman Maitama, Asokoto da Wuse, duk zan karbe.

Inda rusau zai shafa a Abuja

A baya ana da labari Rusau zai iya shafar mazauna Dei Dei, Durumi, Dutse, Garki da yankin Apo, Kubwa, Lokogoma, Lugbe, Mabushi da Mpape.

Mutanen Nyanya, Piya Kasa, Gishiri, Gwagwalape, Idu, Jabi, Kado, Karshi, Karu sai sun hada da addua’a domin gwamnati za ta ruguza gine-gine.

Asali: Legit.ng

Online view pixel