Bankin CBN Ya Bayyana Masu Kawo Cikas Kan Daga Darajar Naira A Najeriya

Bankin CBN Ya Bayyana Masu Kawo Cikas Kan Daga Darajar Naira A Najeriya

  • Babban Bankin Najeriya, CBN ya saka takunkumin fita ga masu gunadar da bankuna kasashen ketare don amsa tambayoyi
  • Ana zargin masu gudanar da bankuna da karya darajar Naira don biyan bukatar kansu da iyalansu inda su ke kwasar Dalolin zuwa waje
  • Masu gudanar da bankunan na cin riba matuka a duk lokacin da darajar Naira ta fadi yayin da Dala ke tashi a kasuwanni

FCT, Abuja – Babban Bankin Najeriya (CBN) ya hana daraktocin bankuna fita kasar ketare daga 5 zuwa 15 ga watan Agusta don amsa wasu tambayoyi kan fadurar Naira a kasar.

Takunkumin na zuwa ne bayan zarginsu da kwasar Daloli zuwa kasashen ketare tare da karya farashin Naira don biyan bukatar kansu, Legit.ng ta tattaro.

Bankin CBN ya fallasa masu amfani da karfinsu wurin karya darajar Naira
Bankin CBN Ya Saka Takunkumi Ga Masu Kawo Cikas A Daga Darajar Naira. Hoto: Boy_Anupong.
Asali: Getty Images

Rahoton The Nation ta tabbatar cewa manyan masu bankuna su na siyar da Daloli da tsada ganin yadda CBN ya kawo sabbin tsare-tsare.

Kara karanta wannan

Jerin Jiga-Jigan Ministoci 9 da Zasu Fayyace Nasarar Shugaba Tinubu Ko Gazawa da Dalilai

Wani takunkumi CBN ya kakaba?

Wata majiya ta tattaro cewa wadanda ke cin moriyar faduwar darajar Naira su ne manyan masu gudanarwa a bankuna inda su ke rike ta ko siyarwa lokacin da su ka dama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauye-sauyen da shugaban kasa, Bola Tinubu ya kawo don daga darajar Naira ya saka shugabannin bankunan siyar da Dalolin ga iyalansu ko kuma abokai wanda hakan ke saka kwastomomi shan wahala kafin samu.

Rahotannin sun tattaro cewa an dage takunkumin hana shugabannin bankunan fita kasashen ketare a ranar 15 ga watan Agusta.

Kakakin bankin CBN, Isa AbdulMumin ya ce ba shi da masaniya a kan takunkumin hana fita da aka kakaba wa shugabannin bankunan.

Meye CBN ya ce kan takunkumin?

Ya ce:

“Ban ga wasikar da aka rubuta da ta ke tabbatar da takunkumin hana fita kasar wajen ba.”

Kara karanta wannan

Meye zai faru? Shugaban matasan PDP ya bayyana kwarin gwiwar tsige Tinubu a mulki

Har ila yau, darajar Naira ta kara sama a kan Dala a ‘yan kwanakin nan a kasuwanni na hukuma da kuma ta bayan fage.

Naira ta yi sama ne yayin da kamfanin NNPC ya ciwo bashin Dala biliyan 3 daga bankin Afrexim don farfado da darajar Naira a Najeriya.

NNPC Ya Ciwo Bashin Dala Biliyan 3 Don Inganta Naira

A wani labarin, Kamfanin Mai na NNPC ya karbo bashin Dala biliyan 3 a bankin Afrexim na kasar Masar.

Wannan na zuwa ne bayan darajar Naira ta fadi kasa warwas a kasuwanni idan aka kwatanta da Dalar Amurka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel