Sanata Aduda Ya Samu Nasarar Zama Sabon Shugaban PDP Na Jihar Kogi

Sanata Aduda Ya Samu Nasarar Zama Sabon Shugaban PDP Na Jihar Kogi

  • Jam'iyyar PDP ta naɗa shugaban jam'iyya na rikon kwarya a jihar Kogi da Sakatare bayan karewar wa'adin zababbun mambobin NWC
  • Sakataren tsare-tsare, Umar Bature ne ya sanar da haka, inda ya bayyana sunayen mambobin kwamitin rikon kwarya mai ɗauke da mutum 14
  • PDP ta amince da naɗa tsohon sanatan Abuja, Philip Aduda a matsayin shugaban riƙo da kuma George Daika a matsayin Sakatare

Kogi state - Tsohon Sanata mai wakiltar mazaɓar birnin tarayya Abuja, Sanata Philip Aduda, ne zai jagoranci kwamitin riƙon kwarya na jam'iyyar PDP reshen jihar Kogi.

Jaridar Tribune Online ta rahoto cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sakataren tsare-tsare na jam'iyyar PDP ta ƙasa, Honorabul Umar Bature.

PDP ta kafa kwamitin rikon kwarya a jihar Kogi.
Sanata Aduda Ya Samu Nasarar Zama Sabon Shugaban PDP Na Jihar Kogi Hoto: tribuneonline
Asali: UGC

Sanarwan ta ce kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC-PDP) ga amince da kafa kwamitin riƙon kwarya mai ƙunshe da mutum 14 bayan tattaunawar neman shawari da masu ruwa da tsaki a jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Shin Jam'iyyun PDP, NNPP Da LP Na Shirin Dunkulewa Waje Daya? Peter Obi Ya Bayyana Gaskiya

Bature ya bayyana cewa kwamitin, "Zai ci gaba da jan ragamar tafiyar da harkokin jam'iyyar PDP a jihar biyo bayan ƙarewar wa'adin zaɓaɓɓun mambobin NWC na Kogi."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jerin mutanen da suka shiga kwamitin riƙon kwarya

Sanata Aduda ne zai jagoranci kwamitin a matsayin muƙaddashin shugaban PDP reshen jiha yayin da Honorabul George Daika ya zama Sakataren jam'iyya.

Sauran mambobin kwamitin sun ƙunshi, Honorabul Joshua Adejoh, Sunday Shugaba, Paul Ukwenya, Honorabul Gbenga Olorunnipa, Honorabul MO Sule, Chief Dayo Akande da Honorabul Siyaka Uchunaye.

Audu Idris, Honorabul Sheidu O Abara, Bilkisu Onusagba, Abiola Olajubu da kuma Grace Atawodi duk suna cikin mambobin kwamitin rikon PDP a jihar Ƙogi da ke Arewa ta Tsakiya.

Nan gaba za a rantsar da kwamitin a ɗakin taron kwamitin zartarwa na jam'iyyar PDP ta ƙasa (NEC) wanda ke Wadata Plaza a babban birnin tarayya Abuja, Dailypost ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sabuwar Rigima Ta Kunno Kai a Jam'iyyar PDP, Babban Jigo Ya Maka Damagun, NWC da NEC a Kotu

Wannan na zuwa ne awanni kaɗan bayan jigon PDP ya shigar da ƙarar shugaban jam'iyya na ƙasa, Umar Damagun, NWC da NEC a gaban Kotu.

Shugaba Tinubu Zai Tsamo Yan Najeriya Miliyan 136 Daga Kangin Talauci

A wani rahoton na daban kuma Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na shirin tsamo yan Najeriya miliyan 136 daga ƙangin talauci da samar da ayyuka 10m.

Ministar harkokin jin ƙai da yaye talauci, Dakta Betta Edo ce ta bayyana haka yayin da ta shiga ofis a karon farko ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel