Shugaba Tinubu Zai Tsamo Yan Najeriya Miliyan 136 Daga Kangin Talauci

Shugaba Tinubu Zai Tsamo Yan Najeriya Miliyan 136 Daga Kangin Talauci

  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na shirin tsamo yan Najeriya miliyan 136 daga ƙangin talauci da samar da ayyuka 10m
  • Ministar harkokin jin ƙai da yaye talauci, Dakta Betta Edo ce ta bayyana haka yayin da ta shiga ofis a karon farko ranar Litinin
  • Ta ce ma'aikatar zata bullo da tsare-tsaren da zasu yi tasiri a rayuwar yan Najeriya kuma su yaye musu damuwa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Ministar jin kai da kawar da fatara, Betta Edu ta bayyana shirin shugaban kasa, Bola Tinubu, na tsamo 'yan Najeriya kimanin miliyan 136 daga kangin talauci.

Dakta Bettta Edu ta bayyana cewa shugaban ƙasa ba zai lamurci ƙaruwar talakawa ba a ƙasar nan, lamarin da ya jima ya ci wa gwamnati tuwo a kwarya.

Shugaba Tinubu da ministar jin ƙai.
Shugaba Tinubu Zai Tsamo Yan Najeriya Miliyan 136 Daga Kangin Talauci Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Sabuwar ministar ta yi wannan furucin ne yayin da ta shiga ofishinta a ma'aikatar jin ƙai da yaƙi da talauci karon farko bayan rantsuwar kama aiki a Abuja ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Sabon Ministan Shugaba Tinubu Ya Ce Zai Yi Aiki Kamar Magini a Yayin Da Ya Shiga Ofis

The Nation ta rahoto Ministar na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Shugaban ƙasa yana da ajanda kuma mai sauƙi ce; sabunta fatan 'yan Najeriya. Akwai ayyuka da yawa da za a yi. Na dau lokaci na yi bincike kan wasu bayanai kuma na ga cewa muna da talakawa kusan miliyan 136."
“Bari mu dauka da gaske cewa bayanan da muke da su daidai ne, muna da ‘yan Najeriya miliyan 200, wanda ina ganin mun fi haka, miliyan 136 ciki suna fama da talauci, Tinubu ba zai amince da haka ba."

Ta ce shirin fitar da ‘yan Najeriya miliyan 136 daga kangin talauci abu ne da zai yiwu, kuma za a yi shi ne mataki-mataki, shugaban ƙasa na tare da shirin ɗari bisa ɗari.

Tinubu zai samar da ayyukan yi miliyan 10

Misis Edu ta kuma bayyana cewa ma'aikatar jin ƙai zata samar da ayyukan yi miliyan 10 ga 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

"Ba Zan Yi Karya Domin Kare Gwamnatin Tinubu Ba" Sabon Minista Ya Yi Magana Mai Jan Hankali

A rahoton Vanguard, Edu ta ƙara da cewa:

"Za mu samar da mafi ƙaranci ayyuka miliyan 10 daga wannan ma'aikatar.
"Kamar yadda muke samun abokan hulɗa masu son ci gaba suna shigowa kuma suna daukar mutane su yi musu ayyukan jin kai na gajeren lokaci da sauran su, mu ma za mu samar da wadannan ayyuka ga ‘yan Najeriya."

"Ba Zamu Faɗi Karya Domin Kare Gwamnati Ba' Sabon Minista

A wani labarin kuma Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Muhammed Idris ya shiga Ofis a karon farko bayan rantsuwar kama aiki.

Idris ya bayyana cewa ma'aikatarsa ba zata rungumi yin ƙarya ba domin kare gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel