“Dalilin Da Yasa Aka Daina Ganinmu Tare Da Maryam Yahaya”, Amal Ta Fasa Kwai

“Dalilin Da Yasa Aka Daina Ganinmu Tare Da Maryam Yahaya”, Amal Ta Fasa Kwai

  • Jarumar Kannywood, Amal Umar ta bayyana dalilin rashin ganinsu tare da Maryam Yahaya kamar yadda aka saba a baya
  • Amal ta ce babu wani abu da ya shiga tsakaninsu suna nan kamar dai Hassana da Hussaina
  • Jarumar ta ce kawai dai sabgogin gabansu ne ya sha kansu kasancewar yanzu kowaccensu ta mallaki hankalinta

Shahararriyar jarumar masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Amal Umar ta bayyana dalilin rashin ganinsu tare da takwararta kuma aminiyarta, Maryam Yahaya.

Ana dai yi wa matasan jaruman biyu da taurarinsu ke haskawa a masana'antar fim din lakabi da 'Hassana da Hussaina' saboda kusanci da shakuwarsu.

Amal ta ce har yanzu Maryam Yahaya Hassanarta ce
“Dalilin Da Yasa Aka Daina Ganinmu Tare Da Maryam Yahaya”, Amal Ta Fasa Kwai Hoto: Facebook/Amal Umar/Skabash!
Asali: UGC

Sai dai a yan baya-bayan nan ba a ganinsu tare kamar da lamarin da ya sa shahararriyar jaruma Hadiza Aliyu Gabon yi wa ita Amal Tambaya kan haka a yayin da ta bayyana a shirinta na 'Gabon's Room Talk Show'.

Kara karanta wannan

"Badakalar Miliyan 40": Amal Umar Ta Bayyana Gaskiyar Abun da Ya Wakana Tsakaninta Da Tsohon Saurayinta

Abun da yasa ba a ganina tare da Maryam Yahaya, Amal

Da take bayar da amsa, jaruma Amal ta ce har yanzu Maryam na nan a matsayinta na Hassanarta, sai dai ta ce yanayi da sabgogin gabansu ne yasa ba a ganinsu tare kamar da.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta kuma bayyana cewa Maryam na da kawaye da yawa wanda tarayyarsu yasa su wadancan suna ganin kamar bata basu damar sakewa, inda hakan yasa ta dan ja baya domin ta basu sarari su wataya.

Ta ce:

"Har gobe Hassana da Hussainan ne. Abun da ya faru ba'a ganinmu tare da komai tare muke yi kafin mu dan waye don rana daya aka fara sa mana kamara tare da ita, fim daya muka fara yi amma daga baya ba'a ganinmu tare.
"Kin san ni bani da kawaye, don ko yanzu kika ce min na gaya maki kawayena guda biyu ko uku gaskiya ba zan iya gaya maki ba amma dai wadanda nake aiki da su in an hadu kawayena ne amma idan an rabu kowa ya kama kansa, amma ban da wasu mutum biyu haka da zan ce maki kawayena.

Kara karanta wannan

100 sun mutu: Yanzu haka 'yan Boko Haram da ISWAP suna can suna ta kwabza yaki a Borno

"Ita kuma Maryam gaskiya tana da kawaye, kuma a wancan lokacin akwai wasu kawayenta da suke ganin kamar idan ina kusa da ita kamar ina hana su mu'amala da ita ko kuma ina hanasu su shiga jikinta. Tun a wannan lokacin sai na fara kyaleta.
"Kuma kin san idan mutum ya fara girma watakila tana da abubuwanta, sabgoginta nima ina da nawa kuma abunmu ba lallai ne ya zo iri daya ba toh shiyasa ba a ganinmu tare amma har yanzu, har gobe ita ce Hassanata."

Amal Umar ta bayyana gaskiya kan zargin da ake mata na damfara

A baya mun ji cewa Amal Umar, ta bayyana gaskiyar lamari kan zargin da wani tsohon saurayinta ke mata na cinye masa kudi.

Idan dai za ku tuna, jaruma Amal na fuskantar tuhuma na damfarar wani tsohon saurayinta kudi wanda yawansu ya kai kimanin Naira miliyan 40.

Asali: Legit.ng

Online view pixel