Latest
A yayin da take shirin gudanar da zaben kananan hukumomi, gwamnatin jihar Yobe karkashin Gwamna Mai Mala Buni ta rusa shugabannin riko 17 da kansilolinsu.
An shiga wani irin yanayi bayan rasuwar tsohon sanata a jihar Enugu, Ayogu Eze wanda ya wakilci Enugu ta Arewa a Majalisar Dattawa daga shekarar 2007 zuwa 2015.
Wasu jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a shiyyar Arewa ta Tsakiya, sun bukaci Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus daga shugabancin jam'iyyar.
Babbar Kotun Tarayya ta yi fatali da korafin da aka shigar kan Ministar Al'adu, Hannatu Musawa game da rashin kammala bautar ƙasa yayin da aka naɗa ta mukami.
A yayin da gwamnatin Abba Yusuf ke karin haske kan kokarin da take yi na magance karancin ruwa a Kano, ta ce tana kashe akalla N1.2bn duk wata domin samar da ruwa.
Wani malamin addinin kirista ya jawo cece-kuce a Twitter bayan da ya wallafa wani bidiyo inda ya ke yin bushara da cewa za ayi tashin alkiyama 25 ga Afrilu, 2024.
Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da cewa jami'an ta sun samu nasarar hallaka wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar.
Karancin mai ya janyo dogayen mai a jihohin Najeriya ciki har da Kano, Gombe, Adamawa, Lagos, Anambra da babban birnin Abuja. Masu ababen hawa sun shiga matsala
Mazauna kauyen Allawa da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja sun shiga fargaba bayan sojoji sun tattare kayansu a kauyen sun fice da safiyar yau Alhamis.
Masu zafi
Samu kari