Muna Kashe N1.2bn a Duk Wata Domin Samar da Ruwa a Kano, in Ji Gwamnatin Abba

Muna Kashe N1.2bn a Duk Wata Domin Samar da Ruwa a Kano, in Ji Gwamnatin Abba

  • A yayin da matsalar karancin ruwan sha ke addabar Kano, gwamnatin jihar ta fito ta yi karin haske kan kokarin da take yi kan lamarin
  • A cewar kwamishinan albarkatun ruwa na jihar, Ali Makoda, gwamnatin jihar na kashe Naira biliyan 1.2 a kowanne wata kan ruwan sha
  • Ya kuma nuna bayyana cewa Gwamna Abba Yusuf ya kulla yarjejeniya da gwamnatin Faransa domin gina cibiyar samar da ruwa a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa tana kashe akalla Naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha a cikin birnin Kano.

Gwamnatin Abba Yusuf ta yi magana kan gyara matsalar ruwa a Kano
Gwamnatin jihar Kano na kashe akalla N1.2bn a kowane wata domin samar da ruwa. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar, Ali Makoda ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Dama ta samu: Yadda ’yan Najeriya za su iya yin karatu kyauta a kasar Birtaniya

Ya ce ana kashe kudin wajen sayen dizal na N400m, sinadaran gyara ruwa na N387m da kuma biyan kudin wutar lantarki da N280m, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Muna kokarin gyara matsalar karancin ruwan sha a babban birnin jihar da kewaye. Nan da 'yan kwanaki kadan matsalar za ta kare”

- Ali Makoda.

Matsalar karancin ruwa a Kano

Kwamishinan ya danganta matsalar karancin ruwan sha da ake fama da ita a jihar da tsofaffin kayan aiki, musamman a cibiyar kula da samar da ruwa ta Tamburawa.

"Yawan zafin rana a cikin babban birnin yana dumama jiki ta yadda mutane za su rika shan ruwa mai yawa, wanda hakan na jawo saurin karewar ruwa."

- In ji kwamishinan.

Makoda ya yi Allah-wadai da gwamnatin jihar da ta gabata kan yadda ta yi watsi da harkar ruwa, inda ya ce kashi 20% ne kawai ta cimmawa na bukatun jama'a.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Majalisa ta tura bukata ma'aikatar kudi kan binciken badakala

Kokarin gwamnatin Abba kan ruwa a Kano

Domin magance kalubalen samar da ruwa na dogon lokaci, Makoda ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta yi wani hadin gwiwa da gwamnatin kasar Faransa.

Kamar yadda rahoton Arise TV ya nuna, Gwamnatin Kano da ta Faransa za su zuba jarin Yuro miliyan 63.4 wajen gina katafariyar cibiyar kula da ruwa ta uku a jihar Kano.

Kwamishinan ya jaddada cewa:

"Gwamna Abba Yusuf yana daukar kwararan matakai domin wadatar da ruwa da suka hada da ware makudan kudade domin cimma wannan buri”.

Gwamnan Kano ya isa kasar Amurka

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya isa birnin Washington DC da ke Amurka domin halartar taro kan matsalar tsaron Arewa.

Gwamnan ya wanda bayyana cewa ya hadu da sauran gwamnonin jihohin Arewa da aka gayyata taron, ya ce taron zai taimaka wajen kawo karshen ta'addanci a Arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel