Karancin Fetur: Dogayen Layin Mai Sun Dawo Abuja, Kano da Wasu Jihohi

Karancin Fetur: Dogayen Layin Mai Sun Dawo Abuja, Kano da Wasu Jihohi

  • An wayi garin Alhamis da ganin dogayen layin mai a wasu jihohin kasar nan ciki har da Kano, Gombe, Anambra da babban birnin tarayya Abuja
  • Rashin samun man ya kara ta'azzara farashin ababen hawa yayin da wasu gidajen man su ka ku budewa ballantana su sayarwa masu bukata man fetur
  • Sakataren kungiyar masu kasuwancin man fetur ta kasa (IPMAN), John Kekeocha ya ce za su zauna da kamfanin mai na NNPCL domin gano bakin matsalar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru shida. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-An wayi garin Alhamis da ganin dogayen layi a wasu jihohin kasar nan ciki har da Kano, Gombe, Nassarawa, Neja, Sokoto, Anambra da babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Tsaro: Gwamatin Sokoto ta tumbuke hakimai 15, an canzawa wasu masarautu

Wasu gidajen man kuma sun kasance a rufe, yayin da masu ababen hawa ke ta fafutukar samun mai domin gudanar da ayyukansu na yau da kullum.

Wani rahoton da Punch News ta ruwaito ya bayyana cewa mutane da dama suna takawa saboda rashin ababen hawan da ke can su na bin layin mai.

Wasu daga gidajen man da ake sayar da fetur da dan tsada na naira dari 800 ba su da dogon layin wuraren da ake sayarwa a kan naira 620.

Ana sayar da man a kan naira 800 a wasu wuraren
Wuraren da ake sayar da tsada babu layi sosai
Asali: Original

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Motoci, babur na jimawa a layin fetur

Adamu Musa Kankarofi, wani mai adaidata sahu ne a jihar Kano, kuma ya bayyanawa Legit Hausa yadda ya dade a layi kafin samun mai a gidan mai na NNPCL da ke titin Ibrahim Taiwo.

Ya ce tun wurin 8.00 na safe ya hau layi, kuma ya samu shan mai da misalin karfe 11.00 a kan N620 kowace lita.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano gidan burodin 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno

Rashin man ya jawo dogayen layi a wasu gidajen mai a Kano
Masu adaidata sahu na bin layin mai
Asali: Original

A jihar Gombe, masu ababen hawa na bin layi na tsawon awa biyu, kuma sun sayi mai a kan N755 kowace lita.

Duk da karin farashi a wasu gidajen mai, zagayen da Legit Hausa ya yi ya gano wasu gidajen mai a Kano sun rufe.

Gidan man NNPCL a Kano
Gidan man NNPCL kan rufe gidan man sai an kammala sallamar wadanda ke ciki
Asali: Original

Rahoton ya bayyana cewa an rufe gidajen mai da dama a Zuba, da ke jihar Neja, da wasu da ke titin Arab a Kubwa, Abuja.

Fetur: “Za mu tattauna da NNPCL,” Kekeocha

Sakataren masu kasuwancin man fetur na kasa (IPMAN), Cif John Kekeocha ya bayyana cewa ba su san dalilan karancin man fetur din da ake fuskanta a wasu sassan kasar nan ba.

Sai dai ya ce akwai karancin man fetur a kasar, kuma a yau za su duba batun da kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) domin shawo kan matsalar.

“Karancin man fetur zai kau,” Kyari

Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), ya tabbatarwa 'yan kasar nan cewa, nan gaba kadan zai magance karancin man fetur a Najeriya.

Kara karanta wannan

70% na fursunoni a Kano na jiran shari'a, suna samun ilimi a daure

Babban Babban jami'in gudanarwa na kamfanin, Mele Kyari ne ya bayyana haka sai dai ba zai bayar da tabbacin yankewar karancin mai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel