“Mun Ji Shiru”: An Caccaki Faston da Ya Ce Za a Busa Kaho a Ranar 25 Ga Afrilun 2024

“Mun Ji Shiru”: An Caccaki Faston da Ya Ce Za a Busa Kaho a Ranar 25 Ga Afrilun 2024

  • Wani malamin addini da ya yi busharar cewa za ayi tashin alkiyama a yau, 25 ga Afrilu, 2024 ya jawo cece-kuce a soshiyal midiya
  • A 'yan makonnin da suka gabata ne Faston ya yi iƙirarin cewa ya sami wahayi kan ranar busa kaho inda ya nemi kowa ya shirya kansa
  • Sai dai masu amfani da yanar gizo sun jefe shi da tambayoyi masu ban dariya tare da tambayar ko an dage ranar da za a tashi duniyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ma'abota amfani da shafukan sada zumunta sun caccaki wani Fasto da ya wallafa bidiyo a yanar gizo na iƙirarin cewa za ayi tashin alkiyama a yau, 25 ga Afrilu, 2024.

Kara karanta wannan

Malaman musulunci sun shiga gargadin DisCos a kan lalacewar wutar lantarki

'Yan Najeriya sun caccaki Fasto da ya yi bushara kan ranar tashin alkiyama
Fasto ya yi ikirarin cewa za ayi tashin alkiyama a ranar 25 ga Afrilu, 2024. Hoto: @prophetmetu/X
Asali: Twitter

A ranar 19 ga watan Maris, malamin addinin ya aika da sako ta hanyar shafinsa na X yana mai gargadin jama'a da kowa ya shirya kansa domin zuwan wannan ranar.

"25 ga Afrilu za a busa kaho" - Fasto

Sai dai malamin addinin da aka bayyana a matsayin @prophetmetu a kan X ya gamu da gamonsa bayan da 'yan Najeriya suka yi masa lakabi da 'malamin karya.'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu amfani da yanar gizon sun yi masa ba'a da cewa ranar 25 ga watan Afrilu da ya yi ikirarin za a busa kaho ta zo, amma har yanzu sun ji shiru.

Amma malamin addinin ya kara jaddadawa a cikin wani faifan bidiyo cewa wahayin da aka yi masa babu makawa zai tabbata tare da yin gargaɗi ga jama'a.

Ya ce:

Kara karanta wannan

Neja: An shiga fargaba bayan 'yan bindiga sun sake hallaka sojoji tare da sace Kyaftin

“Wahayin da aka yi mani babu nukusani a ciki, kuma komai ya bayyana gare ni cewa 25 ga watan Afrilu, 2024 ne za ayi tashin alkiyama."

'Yan Najeriya sun caccaki Fasto

'Yan Najeriya sun shiga sashen sharhi na bidiyon da ya wallafa sun yiwa malamin ba'a tare da tambayar ko an dage ranar ne.

@Hon_owolewa ya yi martani:

"Ya ake ciki ne wai, anya ka ga komai a wahayin nan kuwa ko har an yi tashin alkiyamar ne ba mu sani ba?"

@holycenter101 ya ce:

"25 ga wata dai ta zo, me ya faru ne har yanzu ba a busa kaho ba, ko wahayin naka ya zo da gardama ne?"

@FlashObaji ya yi martani:

"Wanda ya sha ya bugu ne wai zo yana maganar wahayi ku yarda?

@postbyox ya ce:

"Wai ya muka ji shiru ne, za a tashi duniyar ne yau ko an dage sai wata rana a gaba?"

Kara karanta wannan

Mulkin Tinubu ya dara shekaru 16 a PDP ta fuskar tsaro, Hadimin Tinubu

"Shekarar 2028 za a busa ƙaho" - Bature

A wani labarin makamancin wannan, Legit Hausa ta ruwaito cewa wani Bature a Amurka ya ce nan da shekarar 2028 za a yi tashin alkiyama.

Mutumin mai suna Leslie Southam wanda yake da shekara 53 a lokacin da ya yi wannan maganar a 2021, ya ce zai killace kansa a waje daya har a tashi duniyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel