Yawan Mutuwa: An Fara Zargin Abin da Ya Haddasa Mutuwa Barkatai a Kano

Yawan Mutuwa: An Fara Zargin Abin da Ya Haddasa Mutuwa Barkatai a Kano

  • Gwamnatin Kano ta bayyana cewa ta fara binciken dalilan yawaitar mutuwa da ake samu a yan kwanakin nan a kauyuka da biranen jihar
  • Kwamishinan lafiya na jihar, Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan ga manema labarai yau a Kano, inda ya shawarci al'umma
  • Ya ce duk da ana bincike, amma ana zargin zazzabin cizon sauro da tsananin zafi da janyo cututtukan da ke janyo yawaitar rashe-rashen

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru shida. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano-Ma’aikatar lafiya ta Kano ta ce ta na bincike kan yawan mace-macen da ake samu a jihar Kano a ‘yan kwanakin nan.

Kwamishinan Lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana haka ta cikin wani sakon murya da jami'in hulda da jama’a na ma’aikatar, Ibrahim Abdullahi ya rabawa manema labarai.

Kara karanta wannan

Kasar Saudiyya ta sauke kabakin arzikin dabino ga mazauna Kano

Ana ci gaba da bincike kan dalilan yawaitar mutuwa a Kano
Ma'aikatar lafiya ta Kano na zargin tsananin zafi da haddasa yawan mace-mace a jihar Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A kwafin sakon muryar da Legit Hausa ta saurara, kwamishinan ya ce akwai bukatar al’umma su dauki matakan kare lafiyarsu saboda tsananin zafin da ake fuskanta a Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana fargabar shanyewar barin jiki a Kano

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ya bayyana fargabar tsananin zafin da ake fama da shi na tsotse ruwan jikin mazauna Kano.

Ya ce wannan na daga matsalar da ake tunanin na janyo mutane su na faduwa suna mutuwa a jihar.

Amma kwamishinan ya ce ana zurfafa bincike, sai dai daga matsalar da ake zargi akwai zazzabin cizon sauro, sankarau da tsananin ciwon kai.

A kalamansa;

“Tsananin zafin na janyo cutar shanyewar barin jiki saboda karancin jini da ruwa da ake samu a jikin mutum sakamakon tsananin zafin, wanda kan iya haifar da matsalar kwakwalwa, musamman ga wadanda suka manyanta, da masu aikin karfi.”

Kara karanta wannan

70% na fursunoni a Kano na jiran shari'a, suna samun ilimi a daure

An shafe wata guda ana zafi a Kano

Dakta Labaran ya ce yanayin zafin da ake ciki ya fara ne tun daga watan Maris na wannan shekara, wanda ya sanya karuwar zazzabi da mace-macen.

Kwamishinan ya yi tuni da cewa watanni guda uku na Maris, Afrilu da Mayu, har ma da farkon watan Yuni – watanni ne na ta’azzarar zafin rana, da hakan ke janyo abubuwa masu yawa da suka haɗd da karuwar zazzabin cizon sauro da cutar sankarau.

An zargi Gwamnati da janyo mutuwar mutane

Mun kawo mu ku cewa Phrank Shu'aibu, hadimin tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Tinubu da jefa yan kasar nan cikin yunwa.

'Dan siyasar ya ce yan Najeriya na mutuwa sakamakon talauci da tashe tashen hankula, wanda ya bayyana da abun takaici matuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel