Latest
Wata gobara ta tashi a gidan tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau a cikin daren ranar Lahadi. Gobarar ta lalata wani daki a cikin gidan.
Wani tsagin jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya shigar da kara a gaban hukumar EFCC kan Rabiu Musa Kwankwaso da wasu mutum 13 kan zargin N2.5bn
'Yan kasuwa a Arewacin Najeriya sun yi barazanar daina kai kaya Kudu saboda yadda aka jawo masu asara kwanan nan bayan samun tsaiko da aka yi a kasuwa.
Wata 'yar jarida, ta bankado yadda wani likitan boge ke zubar wa 'yan mata ciki a unguwar Yan-Doya da ke Jos, jihar Plateau a kan N5,000 tare da jefasu a karuwanci.
Wani jigo a babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratuc Party (PDP) ya fadi dalilin da ya sanya jam'iyyar ba ta hukunta tsohon gwamnan Rivers Nyesom Wike ba.
Hukumar FAAN da ofishin Nuhu Ribadu sun hada kai domin rage yawan jami'an hukumomi da ke bincike a filayen jiragen saman Najeriya yayin da fasinjoji ke korafi.
Kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) ta ba kamfanin rarraba wutar lantarki na Enugu wa'adi na daidaita wutar lantarki a yankin Kudu maso Gabas.
An samu sabani tsakanin kungiyoyi biyu na 'yan awaren da ke neman a raba Najeriya gida biyu domin samun damar cin gashin kai sabanin haduwa wuri daya.
Tsohon gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku ya sanar da mutuwar tsohon kwamishinan lafiya a gwamnatinsa, Dakta Innocent Vakkai bayan fama da jinya.
Masu zafi
Samu kari