Taraba: An Shiga Jimami Bayan Tsohon Kwamishina Ya Kwanta Dama

Taraba: An Shiga Jimami Bayan Tsohon Kwamishina Ya Kwanta Dama

  • An shiga jimami a jihar Taraba bayan mutuwar tsohon kwamishinan lafiya a gwamnatin Injiniya Darius Ishaku
  • Marigayin mai suna Dakta Innocent Vakkai ya rasu ne a ranar Juma'a 3 ga watan Mayu a babban asibitin Tarayya a Jalingo
  • Tsohon gwamnan jihar, Darius Ishaku ya tabbatar da mutuwar tsohon kwamishinan inda ya jajantawa iyalansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Taraba - Tsohon kwamishinan lafiya a jihar Taraba, Dakta Innocent Vakkai ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin ya rasu ne a ranar Juma'a 3 ga watan Mayu a babban asibitin Tarayya da ke Jalingo.

Tsohon kwamishinan lafiya a Taraba ya rasu
Tsohon kwamishinan lafiya a jihar Taraba, Dakta Innocent Vakkai ya rasu. Hoto: Dr. Innocent Vakkai.
Asali: Facebook

Wane mukami Vakkai ya rike a Taraba?

Vakkai ya rike muƙamin kwamishina ne a lokacin mulkin tsohon gwamna, Darius Ishaku, Cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

An tafka babban rashi bayan mutuwar tsohon Minista a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da tsohon gwamnan ya fitar inda ya jajantawa iyalan marigayin.

Ishaku ya ce Vakkai na daga cikin mutanen da suka ba da gudunmawa sosai a Majalisar zartarwa a lokacin mulkinsa.

Ya ce ya kadu da samun labarin mutuwar tsohon kwamishinan wanda suka yi aiki tare ba tare da matsala ba.

Mista Vakkai ya rike muƙamin kwamishina daga shekarar 2015 zuwa 2023 a zamanin mulkin Darius Ishaku.

Gwamnan Taraba ya mika sakon jaje

Har ila yau, Gwamna Agbu Kefas ya jajantawa iyalan marigayin game da rashin da aka yi a jihar Taraba.

Kefas ya ce Vakkai ya taka rawar gani lokacin da ya ke kwamishina a jihar musamman a lamarin annnobar Korona.

Ya kuma ba iyalansa musamman matarsa da 'ya'yansa hakuri kan wannan babban rashi da aka tafka a jihar.

Kara karanta wannan

Borno: Gwamna Zulum ya tafka babban rashi yayin da hadiminsa ya rasu

Tsohon Minista ya riga mu gidan gaskiya

A wani labarin, tsohon ministan ilimi a Najeriya, Cif Kenneth Gbagi ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya a jiya Asabar 4 ga watan Mayu.

Gbagi kafin rasuwarsa ya nemi takarar gwamna a jihar Delta karkashin jam'iyyar SDP a zaben 2023 da aka gudanar.

Tsohon gwamnan jihar Delta, Cif James Ibori ya tabbatar da mutuwar tsohon ministan inda ya jajantawa iyalansa kan wannan babban rashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.