Latest
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar fatattakar 'yan ta'adda a jihar Benue bayan sun yi musayar wuta. Jami'an tsaron sun kubutar da mutum biyu.
Gwamnatin tarayya ta yi martani kan wani rahoto da ake yadawa na cewa tana tattaunawa da Amurka da Faransa kan kafa sansanonin sojinsu bayan barin yankin Sahel.
Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da harin da 'yan bindiga suka kai a kauyen Ambe da ke karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna. Rundunar ta ce an kama dan bindiga 1.
Sojojin Nijar sun cafke kasurgumin dan bindigar nan na Najeriya, Kachallah Mai Daji a Illela a lokacin da yake yunkurin satar dabbobi a kan iyakar Najeriya da Nijar.
Gwamnatin jihar Adamawa ta sanar da daukar matakin rufe makarantu a jihar sakamakon barkewar cutar Kyanda a jihar. Hakan na zuwa ne bayan an rasa rayuka.
Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Ƙashim Shettima zai tashi zuwa birnin.Dalas na ƙasar Amurka domin halartar taron kasuwanci na 2024 a birnin Dallas.
Kotun musulinci da ke kano ta saka ranar Alhamis mai zuwa a matsayin ranar cigaba da sauraron daukaka karar da malam Abduljabbar Nasiru Kabara ya shigar.
Gwamnatin jihar Kano ta ce ba gaskiya ba ne cewa za ta kori masu sharar da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta dauka aiki kamar yadda wasu ke yadawa.
Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu ya ce gwamnatocin da suka sjude ne suka jefa Najeriya a matsin tattalin arzikin da take ciki ba Bola Tinubu ba.
Masu zafi
Samu kari