“Babu Laifin Tinubu”: Mataimakin Kakakin Majalisa Ya Magantu Kan Matsin Tattali

“Babu Laifin Tinubu”: Mataimakin Kakakin Majalisa Ya Magantu Kan Matsin Tattali

  • Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu zargi tsofaffin shugabanni da jefa Najeriya a matsin tattalin arzikin da take ciki
  • Kalu ya yi nuni da cewa Bola Tinubu ya karbi kasar tare da matsalolinta kuma yana aiki tukuru domin ganin lamura sun daidaita
  • Tun da fari, shugaban kasar ya aika sakon taya murnar zagayowar ranar haihuwar mataimakin kakakin majalisar wakilan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Abia - Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu ya tabbatar da cewa ba shugaban kasa Bola Tinubu ne ke da alhakin tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya ba.

Benjamin Kalu ya yi magana kan tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya
Benjamin Kalu ya zargi tsofaffin shugabannin da jefa Najeriya a matsin tattalin arziki. Hoto: @OfficialBenKalu
Asali: Twitter

Kalu ya zargi tsofaffin shugabanni

Dan majalisar ya bayyana haka ne a ranar Lahadi bayan ya bakunci marayu, zawarawa, nakasassu da kuma tsofaffi a gidansa da ke jihar Abia a bikin murnar cikarsa shekaru 53 a duniya.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa ya fadi wanda ya 'jawo' tabarbarewar tattalin arziki lokacin Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Nation ta ruwaito mataimakin kakakin majalisar ya bayyana cewa Tinubu yana kokari matuka wajen gyara kura-kuran da gwamnatocin baya suka yi.

A matsayar Kalu, tsofaffin shugabannin kasar ne suka haifar da matsalolin tattalin arziki da ake fama da su a halin yanzu a Najeriya.

"Tinubu na son tsaftace Najeriya" - Kalu

Kalu ya ce:

“Wahalhalun da muke ciki ba laifin Bola Tinubu bane, tarin kura-kuran gwamnatocin da suka gabata ne da kuma yadda suka karkatar da abubuwa a mulkinsu.
"Tinubu yana son tsaftace Najeriya ne domin mu samu damar yin rayuwa mai kyau da za ta dore. Mu ci gaba da ba shi goyon baya da karfafa masa gwiwa.”

Ya kuma yi hasashen makoma mai kyau ga al’ummar kasar bayan an kawo karshen tashe tashen hankulan da ake fama da su.

Kara karanta wannan

"Jama'a sun ƙosa a yanzu": Sarkin Musulmi ya kuma jan hankalin shugabanni

Tinubu ya aika sako ga Benjamin Kalu

Tun da fari, shugaban kasa Bola Tinubu ya mika sakon taya murna ga mataimakin kakakin majalisar wakilai Benjamin Kalu bisa zagayowar ranar haihuwar sa.

Shugaban ya yi addu’ar Ubangiji ya kara wa mataimakin kakakin majalisar nisan kwana cikin koshin lafiya, tare da kara masa kwarin gwiwa da nasara a kan hidimar da yake yi wa kasa.

Ajuri Ngelale, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin watsa labarai ne ya fitar da sanarwar a ranar Lahadi, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Gwamnati ta fara raba tallafin N50, 000

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba tallafin N50, 000 ga mutane 200,000 da za su ci gajiyar shirin tallafi na shugaban kasa.

Akalla mutane miliyan guda ne shirin ke da nufin tallafa mawa da jarin N50, 000 kafin nan da karshen watan Mayu, 2024, a cewar ministar masana'antu Dr Doris Uzoka-Anite.

Asali: Legit.ng

Online view pixel