Gwamnatin Kano ta Musanta Shirin Korar Wadanda da Ganduje ya Dauka Aiki

Gwamnatin Kano ta Musanta Shirin Korar Wadanda da Ganduje ya Dauka Aiki

  • Gwamnatin jihar Kano ta musanta zargin shirin korar masu sharar tituna da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta dauka aiki
  • Wannan na kunshe cikin sanarwar da darakta janar din Gwamnan kan yada labarai Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar
  • Injiniya Abba Kabir Yusuf ya kuma yi umarnin a biya masu sharar kudinsu da su ke bin gwamnati cikin gaggawa tare da tabbatar da tsaftace Kano

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni na tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya musanta labarin cewa ana shirin korar masu aikin share tituna da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta dauka aiki.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida ya kaddamar da titi mai hawa 3 a kan kudi ₦15bn a Dan Agundi

Ta cikin wata sanarwar da darakta janar din gwamnan kan yada labarai, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya ce babu kamshin gaskiya cikin batun korar ma'aikatan.

Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ba a kori kowane mai shara daga aiki ba Hoto: Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa
Asali: Facebook

A jawabin da Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na facebook, Gwamna Abba ya ce ba shi da hurumin hana wani samun kudin sayen abincin da zai kai bakin salati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a biya masu sharar Kano kudinsu

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin biyan masu share titunan Kano kudin aikinsu da aka shafe watanni ba a basu ba.

Wannan ya biyo yawan korafin da masu aikin sharar wucin gadin ke yi. Wasu daga cikinsu sun ce an hana su albashin da ya kai na watanni shida.

Sai dai Gwamna Abba ya ce dole ne a gaggauta biyan albashin, kamar yadda Kanofocus ta wallafa.

Kara karanta wannan

'Akwai manyan da ke yi wa gwamnatina makarkashiya', Gwamnan APC ya koka

Ya ce bai ji dadin yadda har yanzu ba a biya ma'aikatan albashinsu ba duk da sahalewarsa.

Haka kuma ya umarci ma'aikatar muhalli ta Kano ta gaggauta tabbatar da an kwashe dukkanin sharar da ke titunan jihar.

Shugaba Tinubu ya amince da karin albashi

A baya kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da karin albashin ma'aikata da kaso 25% da kuma kaso 35%.

Sakataren yada labaran hukumar kula da albashi ta kasa, Emmanuel Njoku ne ya bayyana karin wanda ya shafi 'yan fansho da za a yi musu karin kaso 20% da kaso 28%.

Asali: Legit.ng

Online view pixel