Tashin Hankali Yayin da Wani Matashi, Abdullahi Ya Kashe Matarsa Kan Ƙaramin Abu

Tashin Hankali Yayin da Wani Matashi, Abdullahi Ya Kashe Matarsa Kan Ƙaramin Abu

  • Ƴan sanda sun kama wani magidanci bisa zargin halaka matarsa kan wata ƴar gardama a Akure, babban birnin jihar Ondo
  • Binciken ƴan sanda ya nuna cewa magidancin, Fatai Abdullahi, ya caka wa matar almakashi ne kan faɗan da suka saba yi a koda yaushe
  • Mai magana da yawun ƴan sanda, Funmi Odunlami, ya ce yanzu haka suna tsare da wanda ake zargin kuma za su gurfanar da shi a kotu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Wani magidanci ɗan kimanin shekara 30, Fatai Abdullahi, ya yi ajalin mai ɗakinsa mai suna Morenike kan wani ɗan ƙaramin sabani da ya shiga tsakanin su.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, magidancin ya soka wa matarsa wani ƙarfe har rai ya yi halinsa a Akure, babban birnin jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Bello Matawalle: APC ta fadi manufar masu son ganin EFCC ta binciki minista

Sufetan yan sanda, IGP Kayode.
Wani magidanci ya daɓawa matarsa makami har lahira a jihar Ondo Hoto: Policeng
Asali: Twitter

An tattaro cewa wanda ake zargin ya cakawa naƙasasshiyar matar almakashi ne bayan wata ƴar jayayya, wanda hakan ya zama ajalinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ƴan sandan jihar Ondo ta bayyana cewa magidancin ya aikata wannan ɗanyen aiki ne tun ranar 27 ga watan Maris, 2024.

Yan sanda sun yi bincike

Mai magana da yawun hukumar ƴan sandan jihar, Funmi Odunlami, ya ce wata mata da ke zaune tare da ma'auratan ce ta kai rahoton lamarin.

"Ta faɗa mana cewa ta bar miji da matarsa a gida ranar 26 ga watan Maris, inda ta tafi ibada a coci amma da ta dawo da yammacin wannan rana, sai mijin ya sanar da ita cewa matarsa ta mutu.
"Binciken farko ya nuna ma'auratan na yawan rigima da juna kan zuwan da matar da take domin dubo ɗan da ta haifa da tsohon mijinta. Bayan ya kashe ta mutumin ya rufe gawarta a gida har sai da dare ya yi.

Kara karanta wannan

An harbi wani dan jarida a gidan gwamnatin Kano, bayanai sun fito

"Da aka zurfafa bincike kan gawar matar an gano raunukan da aka mata ta hanyar soka mata wani abu a ciki da wuya. Sannan jami'ai sun gano almakashi cikin jini a wurin da aka yi kisan."

- Funmi Odunlami.

Kakakin ƴan sandan ya ƙara da cewa yazu haka dai wanda ake zargin na hannun ƴan sanda kuma nan ba da daɗewa ba za a gurfanar da shi a gaban ƙuliya.

Barci ya kwashe masu garkuwa a Ondo

A wani rahoton kuma, an ji 'yan sanda sun damƙe ƴan bindiga biyar bayan sun yi garkuwa da matar malamin coci da wasu mutum biyu a jihar Ondo.

Rahotanni sun nuna barci ne ya kwashe masu garkuwar har mutanen da suka sace suka samu nasarar arcewa ba tare da sun sani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel