Latest
Kungiyoyin kwadago sun rage bukatarsu a mafi ƙarancin albashi amma sun ce ba za su karɓi sabon tayin da gwamnatin tarayya ta gabatar na N57,000 ba.
Shugaba Bola Tinubu ya ba ministocinsa sabon umarni kan nunawa yan Najeriya abin da suka tsinana yayin da gwamnati ke cika shekara daya a kan mulki.
Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce akalla jarirai 700 ne ke mutuwa a kowace rana a Najeriya, yana mai jaddada kalubalen da ke cikin yawan mutuwar mata da kananan yara.
Ana kokarin turawa fasto N100,000 an tura masa N1m bisa kuskure, an nemi ya turo sauran kudin yaki. Yan sanda sun kama shi domin cigaba da gudanar da bincike.
Majalisar dokokin jihar Kano za ta yi karatu na uku kan kudirin gyara dokar masarautu da aka kirkiro a mulkin Abdullahi Umar Ganduje, Abba Kabir Yusuf zai sa hannu.
Rundunar ƴan sanda ta kubutar da yaran mamban majalisar dokokin jihar Zamfara waɗanda yan bindiga suka yi garkuwa da su watanni 17 da suka gabata.
Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta yi martani kan zargin da gwamnan jihar Katsina ya yi na cewa jami'an tsaro na hada baki da 'yan bindiga. Ta bukaci ya kawo hujja.
An samu tashin gobara a sakatariyar gwamnatin jihar Kaduna wacce ta tafka barna mai yawa. Gobarar ta shafi wasu ofisoshi da ke wajen sannan ta lalata su.
Babban bankin Najeriya CBN ya umarci ƴan kasuwar hada-hadar musayar kuɗi su sabunta lasisi kuma ya yi sababbin sauye-sauye ga lasisi mai daraja ta farko da ta 2.
Masu zafi
Samu kari