Bayan Watanni 17, Ƴan Sanda Sun Yi Galaba Kan Ƴan Bindigar da Suka Sace Ƴaƴan Ɗan Majalisa

Bayan Watanni 17, Ƴan Sanda Sun Yi Galaba Kan Ƴan Bindigar da Suka Sace Ƴaƴan Ɗan Majalisa

  • Ƴan sanda sun kuɓutar da ƴaƴan ɗan majalisar dokokin jihar Zamfara waɗanda yan bindiga suka sace watanni 17 da suka wuce
  • Mataimakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sanda ta ƙasa, CSP Isuku Victor ne ya bayyana haka a Abuja ranar Laraba
  • Tuni dai rundunar ƴan sandan ta damƙa Maryam da Nana Asma'u ga mahaifinsu, Honorabul Aminu Ardo a birnin tarayya Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Rundunar ƴan sanda a jihar Zamfara ta samu nasarar ceto ƴaƴa mata biyu na mamban majalisar dokoki, Aminu Ardo.

Dakarun ƴan sandan sun kubutar ƴaran ne watanni 17 bayan ƴan bindiga sun yi garkuwa da su a jihar da ke Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da ƴan sanda sun mamaye zauren majalisa yayin da rigama ta kaure

Sufetan ƴan sanda, IGP Kayode.
An ceto ƴaƴan dan majalisar dokokin jihar Zamfara daga hannun ƴan bindiga Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

'Ya 'yan 'dan majalisa Hon. Ardo sun dawo

Mataimakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sanda, CSP Isuku Victor ne ya bayyana haka yayin miƙa yaran ga mahaifinsu a Abuja jiya Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, ƴaƴan ɗan majalisar da aka ceto sun haɗa da Maryam ƴar shekara 10 da kuma Nana Asma'u, ƴar kimanin shekara takwas.

Yadda aka sace ƴaƴan dan majalisar Zamfara

Rundunar ‘yan sandan ta ci gaba da cewa tun farko ƴan bindigar sun sace yaran ne tare da mahaifiyarsu da wasu ‘yan uwansu. 

Amma bisa sa'a, matar ɗan majalisar ta samu nasarar gudowa tare da wasu ƴaƴanta, Nana Asm'au da Maryam kuma suka ci gaba da zama a hannun ƴan ta'addan.

"A watan Nuwamba, 2022, wasu ƴan bindiga a kan babura 60 suka kai farmaki gidan Honorabul Aminu Ardo, ɗan majalisar dokokin jihar Zamfara, suka tafi da matarsa, Hauwa’u da ƴaƴansu huɗu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da jariri tare da mahaifiyarsa a jihar Kaduna

"Hauwa'u ta haihu a hannun ƴan bindiga amma saboda yanayi mara kyau jaririn ya koma. A lokacin damina a 2023 matar ta yi nasarar gudowa tare da biyu daga cikin ƴaƴanta Ummul Khairi and Abdulrazaq."

- CSP Isuku Victor.

Ya jaddada cewa rundunar ƴan sanda ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan Kebbi yana biyan sojoji N500m

A wani rahoton kuma Sanatan jihar Kebbi ya bayyana yadda Gwamna Nasir Idris ke bai wa sojoji N500m duk wata domin magance matsalar ƴan bindiga.

Garba Maidoki ya ce duk da wannan kuɗin da sojojin ke karɓa babu wani abin a zo a gani da suke yi don tsare rayukan mutanen Kebbi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel