Ana Murnar Dala Ta Karye a Kasuwa, Babban Banki CBN Ya Ɗauki Sababbin Matakai
- Yayin da darajar Naira ke ƙaruwa a kasuwa, babban bankin ƙasa CBN ya yi wasu sababbin sauye-sauye domin inganta ayyukan ƴan canji
- CBN ya umarci halastattun ƴan canaji su sabunta lasisin aiki kuma ya cire masu dokar ajiye wasu adadin kudi kafin a ba su lasisi
- Daraktan sashen tsare-tsaren kuɗi na babban bankin, Haruna Mustafa ne ya bayyana haka a wata sanarwa a ranar Laraba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya umarci halastattun ƴan canji da ke kasuwancin hada-hadar kudi su sabunta lasisin aikinsu.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da daraktan tsare-tsaren kudi na CBN, Haruna Mustafa, ya fitar ranar Laraba, 22 ga watan Mayu, 2024.
![](https://netstorage-legit.akamaized.net/images/852df7b3a62fb8d2.jpg?impolicy=cropped-image&imwidth=256)
Kara karanta wannan
Majalisa ta tsige sarkin Kano Aminu Ado Bayero? Shugaban masu rinjaye ya yi bayani
![Gwamnan CBN, Yemi Cardoso. Gwamnan CBN, Yemi Cardoso.](https://netstorage-legit.akamaized.net/images/dce6dd8f89a2c40e.jpg?imwidth=900)
Asali: Twitter
Bankin ya kuma bukaci duk wani ɗan canji ya tabbata ya cika sharuɗɗan nau'in lasisinsa daga nan zuwa watanni shida, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Dukkan ƴan canji da masu tallata ƴan kasuwar hada-hadar kuɗi su cike buƙatar neman sabon lasisi na kowane mataki ko nau'in da ya kwanta masu a rai," in ji CBN.
Bankin CBN ya yi sababbin sauye-sauye
Har ila yau, babban bankin ƙasar nan ya yi wasu sauye-sauye a kundin dokoki da ƙa'idojin ayyukan ƴan canjin da aka amince da su.
Ɗaya daga cikin canje-canjen da bankin ya yi shi ne cire tilascin ajiye N200m ga masu lasisi mai daraja ta farko watau Tier-1.
Haka zalika babban bankin ya jingine ajiye N50m ga masu lasisi mai ƙima ta biyu, cewar rahoton Vanguard.
![](https://netstorage-legit.akamaized.net/images/5f4c4097ea392b6c.jpg?impolicy=cropped-image&imwidth=256)
Kara karanta wannan
"Dalilin da ya sa Kwankwaso, Atiku da Peter Obi ba za su kai labari ba a zaɓen 2027"
CBN ya kuma janye kudin sabunta lasisi na shekara-shekara na N5m ga ƴan canji da ke matakin farko da kuma N1m ga ƴan mataki na biyu.
Sanarwar ta ce:
"Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar da daftarin ka'idojin gudanar da ayyukan ƴan canji a Najeriya a watan Fabrairun 2024, domin jin ra'ayoyin masu ruwa da tsaki.
"Bayan kammala jin shawarwarin masu ruwa a tsaki, a yanzu CBN ya fitar da daftarin ƙa'idojin da aka amince da su domin sa ido kan ayyukan ƴan canji a Najeriya."
Naira ta ƙara daraja a kasuwa
A wani rahoton kuma, an ji kimar Naira ta ƙara sama a kasuwar hada-hadar gwamnati ranar Talata sa'o'i 24 bayan kuɗin Najeriya sun rikita Dalar Amurka.
Rahoton FMDQ mai sa ido kan hada-hadar kuɗi ya nuna cewa Naira ta tashi da N3.31 inda aka yi musayar kowace Dalar Amurka kan N1,465.68.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng