Gwamnatin Abba Za Ta Dawo da Muhammadu Sanusi II Kan Kujerarsa Ta Sarautar Kano

Gwamnatin Abba Za Ta Dawo da Muhammadu Sanusi II Kan Kujerarsa Ta Sarautar Kano

  • Rahotanni sun bayyana cewa ana daf da mayar da Muhammadu Sanusi II kan kujerar Sarkin Kano bayan shekaru biyar da sauke shi
  • A yau Laraba ne majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da kudurin dokar rushe sarakunan jihar Kano tare da mayar da tsarin sarki daya
  • Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa sa hannun Gwamna Abba Kabir Yusuf kawai ake jira domin a Sanusi II ya koma kan kujerarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Rahotannin da ke shigo mana yanzu na nuni da cewa ana neman mayar da Muhammadu Sanusi II kan kujerar Sarkin Kano.

Wannan kuwa na zuwa ne bayan da majalisar jihar Kano ta yi garambawul ga dokar da ta tsige Sarki Sanusi a 2019.

Kara karanta wannan

Abin da ya faru a majalisar Kano inji wanda ya kawo kudirin gyara masarautu

An mayar da Sanusi Lamido II kan kujerar sarautar Kano
Gwamnatin Abba ta dawo da Sanusi II kan kujerar Sarkin Kano. Hoto: @MSII_dynasty
Asali: Facebook

Kamar yadda mai taimakawa gwamnan jihar Kano na musamman, @babarh_ ya bayyana a shafinsa na Twitter a yau Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fadi lokacin rantsar da Sanusi II

Duk da cewa ba a sanar da hakan a hukumance ba, Jaridar Leadership ta samu lamari daga majiya mai tushe cewa an mayar da Sanusi II kan kujerar Sarkin Kano.

A cewar majiyoyi masu inganci:

“Don haka, bayan zartar da wannan doka, za a mayar da Sanusi kan kujerar sarautar Kano kai tsaye. Ba za a tsaya wani tantancewa ba.
Kawai ana jira gwamnan jihar ya sa hannu kan dokar daga yau zuwa gobe Juma'a."

Ana kallon kirkirar sababbin masarautu hudu da gwamnatin Ganduje ta yi a 2019 ya wargaza ikon tsohuwar masarautar Kano, tare da rage ƙarfinta da tasirinta.

Kara karanta wannan

Majalisar Kano ta rusa duka Sarakunan da Gwamnatin Ganduje ta kirkiro a 2019

Ana so a mayar da Sanusi II kan karaga

Tun a baya mun ruwaito yadda kungiyoyi da dama suka rika yin kiraye-kiraye ga majalisar dokokin jihar Kano da ta mayar da Muhammadu Sanusi II kan kujerarsa ta Sarkin Kano.

Ta baya-bayan nan ita ce kungiyar “Yan Dangwalen Jihar Kano” wadda ta yi kira ga mmajalisar da ta rushe tsarin sarakuna 5 a Kano tare da mayar da Sanusi II kan kujerarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel