Rashin Tsaro: DHQ Kalubalanci Gwamna Kan Zargin Sojoji Na Hada Baki da 'Yan Bindiga

Rashin Tsaro: DHQ Kalubalanci Gwamna Kan Zargin Sojoji Na Hada Baki da 'Yan Bindiga

  • Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta yi martani kan zargin da gwamnan jihar Katsina ya yi na cewa wasu gurɓatattun sojoji na haɗa baki da ƴan bindiga
  • DHQ ta ƙalubalanci gwamnan da ya kawo hujjojin da za su tabbatar da zargin da ya yi kan jami'an rundunar sojojin
  • Ta yi nuna da cewa duk da kalaman na gwamnan babu ƙamshin gaskiya a cikinsu, za su iya sanyaya gwiyoyin dakarun sojojin da ke a bakin daga

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta ƙalubalanci gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda da ya tabbatar da zargin da ya yi na cewa wasu jami’an tsaro na taimakawa da cin gajiyar matsalar rashin tsaro a jihar.

Kara karanta wannan

"Dalilin da ya sa Kwankwaso, Atiku da Peter Obi ba za su kai labari ba a zaɓen 2027"

DHQ ta ce tunda ''rundunar sojoji ta ƴan Najeriya ce,'' duk wanda yake da sahihin bayani kan rashin ɗa'a daga jami'anta yana da ƴancin ya sanar da ita.

DHQ ta kalubalanci Gwamna Dikko Radda
DHQ ta kalubalanci Gwamna Dikko Radda na Katsina Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

Radda: Sojoji sun tanka Gwamnan Katsina

Ya yi nuni da cewa, rundunar sojoji tana biyayya ga dukkan zaɓaɓɓun wakilan gwamnati, domin haka suna mutunta dangantakar da ke tsakaninsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba, shi ne ya yi martani kan kalaman gwamnan na jihar Katsina cikin wata sanarwa a jiya Laraba, cewar rahoton jaridar The Nation.

Janar Edward Buba ya ce gwamnan ya yi wannan zargin ne a cikin wata hira da aka yi da shi a ranar, 4 ga watan Mayun 2024.

Martanin DHQ kan Gwamna Radda

Sai dai, Edward Buba ya ce duk da cewa iƙirarin na gwamnan ba gaskiya ba ne, hakan na iya sanyaya gwiwoyin dakarun da ke fafatawa a bakin daga, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sheke 'yan ta'adda 7, sun kwato makamai masu yawa a Kaduna

"Hankalin hedikwatar tsaro ya kai kan wani gagarumin zargi da gwamnan jihar Katsina mai girma Gwamna Dikko Radda ya yi wa sojojin Najeriya."
"Bisa la’akari da maganar mai girma gwamnan jihar Katsina, rundunar sojojin Najeriya ta yanke shawarar cewa ba za ta yi cacar baki da gwamnan ba."
"Maimakon hakan za ta ƙarfafa masa gwiwa ya tunkari mahukuntan rundunar domin tabbatar da zargin da yake yi."

- Manjo Janar Edward Buba

Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta ce dakarun sojoji sun hallaka ƴan ta'adda 715 tare da ceto mutum 465 da aka yi garkuwa da su a faɗin ƙasar nan a cikin watan Afrilu.

Sojojin sun kuma kai hare-haren bam a sansanonin wasu shugabannin ƴan ta’adda da suka haɗa da Nasanda, Babaru, Kamilu Buzaru, Ali Dawud, Bakura Fallujah da Mallam Ari.

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga yanayi yayin da ƴan bindiga suka kashe sojojin Najeriya

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng