Kasashen da Suka Fice Daga ECOWAS Za Su Dawo, Sanata Ndume Ya Bayyana Dalili

Kasashen da Suka Fice Daga ECOWAS Za Su Dawo, Sanata Ndume Ya Bayyana Dalili

  • Dan majalisar wakilan kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta yamma, Sanata Ali Ndume ya ce kasashen da suka fita daga ECOWAS za su dawo
  • Sanata Ali Ndume ya bayyana haka ne yayin hira da manema labarai bayan wani taron majalisar kungiyar da ya gudana a jihar Kano
  • Kasashen Mali, Niger da Burkina Faso sun fita daga kungiyar ECOWAS ne a watan Janairu biyo bayan juyin mulki da soji suka yi a kasashen

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Sananta Ali Ndume ya bayyana yiwuwar dawowar kasashen da suka fice daga kungiyar kasashen yammacin Afrika (ECOWAS).

SAnata NDume
Ali Ndume ya ce Niger, Mali da Burkina Faso za su dawo ECOWAS. Hoto: @Imranmuhdz
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Ali Ndume ya bayyana haka ne a taron majalisar kungiyar ECOWAS a jihar Kano.

Kara karanta wannan

'Dan majalisa ya faɗi yadda suka shirya tsige sarakuna 5 da Ganduje ya naɗa a Kano

Kasashen da suka fice daga kungiyar ECOWAS saboda rikicin siyasa sune Mali, Burkina Faso da jamhuriyar Niger.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Ali Ndume a kan batun ECOWAS

Sanata Ali Ndume ya bayyana wa manema labarai cewa dukkan matakan da ya kamata a dauka domin dawowar kasashen ya kammala, rahoton Pulse Nigeria.

Ga abin da yake cewa:

"An riga an magance babban abin da ya jawo ficewarsu daga kungiyar, a yanzu haka babu takun-saka tsakanin Niger da Najeriya ko sauran kasashen yammacin Afrika. Saboda haka muna tsammanin dawowarsu."

- Sanata Ali Ndume

Dalilin ficewar kasashen daga ECOWAS

Har ila yau Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa kasashen sun fita daga kungiyar ne saboda kin amincewa da juyin mulkin soja da sauran mambobin ECOWAS suka yi.

Sai kuma lafta musu takunkumi da ECOWAS ta yi, amma a halin yanzu an riga a dauke takunkumin karkashin jagorancin shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

'Ba 'yan Jam'iyya ba ne,' matasan APC sun yi martani ga masu son tsige Abdullahi Ganduje

Yaushe kasashen suka fita daga ECOWAS?

A watan Janairun wannar shekarar ne ƙasashen Mali, Niger da Burkina Faso suka sanar da ficewarsu daga kungiyar ECOWAS.

A lokacin da suke fice daga kungiyar, sun bayyana cewa sun dauki matakin ne domin kare mutuncin yan kasarsu.

ECOWAS ta dage takunkumi ga Niger

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar ECOWAS karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta dage takunkumin da ta sakawa Jamhuriyar Nijar da sauran kasashen da sojoji ke mulki.

Hasashe kan rahotanni daga wani taron da ECOWAS ta yi sun nuna cewa an dage takunkumi guda takwas domin rage cikici a yankin Afrika ta yamma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel