Matan Aure Sun Lakadawa Mazajensu Dukan Tsiya a Legas, Adadin Ya Haura 340

Matan Aure Sun Lakadawa Mazajensu Dukan Tsiya a Legas, Adadin Ya Haura 340

  • Akalla mazaje 70 ne matayensu suka lakada masu dukan tsiya da sauran nau'ukan cin zarafi a cikin shekara daya
  • Tsakanin Satumba 2022 zuwa Yuli 2023, an samu akalla maza 340 sun ba da rahoton fuskantar cin zarafi daga matansu
  • Wannan na kunshe ne a cikin rahoton watanni 12 da ma'aikatar mata da kuma hukumar cin zarafin jinsi na Legas suka fitar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Legas - Gwamnatin Legas ta ce akalla maza 70 ne matayensu suka lakada masu dukan tsiya da sauran nau'ikan cin zarafi a cikin shekara daya.

Kwamishiniyar harkokin mata da rage radadin talauci a Legas, Bolaji Cecilia-Dada, ta bayyana hakan a ranar Laraba yayin ganawa da manema labarai.

Kara karanta wannan

'Dan majalisa ya faɗi yadda suka shirya tsige sarakuna 5 da Ganduje ya naɗa a Kano

An fitar da rahoton cin zarafin jinsi a jihar Legas
Rahoto ya nuna mata na lakadawa maza dukan tsiya a jihar Legas. Hoto: fizkes
Asali: Getty Images

Jaridar The Cable ta rahoto Cecilia-Dada ta ce ma'aikatarta karbi korafe-korafe 662 na cin zarafin mata, inda ta ce mata 21 ba su ba da cikakkun bayanai game da halin da suke ciki ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mata sun ci zarafin mazajensu a Legas

Kwamishiniyar ta bayyana cewa:

“Sashin karbar korafe-korafen cin zarafin cikin gidajen aure ya tattara bayanai kanyawan laifuffukan cin zarafin mata daga 2023 zuwa yau.
Ta hanyar ma’aikatar, mazaje 23 ne suka gabatar da kansu domin bayar da rahoton matansu sun lakada masu dukan tsiya, yayin da mata 247 suka ba da rahoton su.”
“Ta hanyar layukanmu na kiran kai tsaye, maza 43 ne suka bayar da rahoton matansu na cin zarafin su, yayin da mata 324 suka ba da na su rahoton."

An ci zarafin maza 340 a 2022/2023

Cecilia-Dada ta ce gwamnatin jihar ta wayar da kan mata a kasuwanni da mazauna yankunan teku a cikin kwanaki 16 na fafutukar yaki da cin zarafin jinsi a shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Kano: Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau ya raba motoci 107 a mazabarsa

Shi ma da yake magana, Titilola Vivour-Adeniyi, sakatariyar zartarwa ta hukumar cin zarafin jinsi a cikin gidajen aure ta Legas (DSVA), ta ba da nata rahoton, in ji rahoton Tribune Online.

Titilola Vivour-Adeniyi, ta ce tsakanin Satumba 2022 zuwa Yuli 2023, an samu akalla maza 340 sun ba da rahoton fuskantar cin zarafi daga matansu.

Jarirai 700 ke mutuwa kullum a Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya ce kalla jarirai 700 ne suke mutuwa a kullum a Najeriya, mafi yawa a kasashen Afrika.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke kaddamar da wata cibiyar PSA ta sarrafa iskar Oxygen a asibitin tunawa Yusuf Dantsoho domin rage mace-macen jarirai a Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel