Kotu Ta Yi Hukunci Kan 'Yancin Dalibai Mata Musulmai Su Sanya Hijabi

Kotu Ta Yi Hukunci Kan 'Yancin Dalibai Mata Musulmai Su Sanya Hijabi

  • Bayan shekara shida da shigar da ƙara daga ƙarshe kotu ta yi hukunci kan shari'ar ƴancin ɗalibai mata musulmai na makarantar 'International School' na sanya hijabi
  • Kotun ta amince ɗaliban na makarantar wacce ke cikin jami'ar Ibadan da su sanya hijabi a saman kayan makarantarsu
  • Alƙalin kotun wanda ya yanke hukunci kan shari'ar Moshood Ishola ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba kowa ƴancin yin addininsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Oyo - Babbar kotun jihar Oyo, da ke Ibadan ta yanke hukuncin cewa ɗalibai mata musulmai na makarantar 'International School' ta jami'ar Ibadan, su na da damar sanya hijabi a saman kayan makarantarsu.

Alƙalin kotun mai shari’a Moshood Ishola ya ce ƴancin yin addini yana cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da ƴan sanda sun mamaye zauren majalisa yayin da rigama ta kaure

Kotu ta yi hukunci kan 'yancin mata su sanya hijabi a Oyo
Kotu ta amince dalibai mata musulmai na makarantar jami'ar Ibadan su sanya hijabi Hoto: UniIbadan UniIbadan
Asali: Facebook

Da yake yanke hukunci a ƙarar a ranar Laraba, alƙalin ya ce hukuncin nasa yana da nasaba da hukunce-hukuncen da Kotun Ƙoli ta yanke a baya, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su wa suka shigar da ƙarar hijabi?

Wasu ɗaliban makarantar tare da goyon bayan iyayensu, suka shigar da ƙarar hukumar gudanarwar makarantar a shekarar 2018, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Sun haƙiƙance cewa suna da ƴancin sanya hijabi a saman kayan makarantarsu.

Waɗanda suka shigar da ƙarar sun haɗa da Faridah Akerele, Aaliyah Dopesi, Akhifah Dokpesi, Raheemah Akinlusi, Imam Akinoso, Hamdallah Olosunde da Aliyyah Adebayo.

Sauran su ne Moriddiyah Yekinni, Ikhlas Badiru, Mahmuda Babarinde, da Fareedah Moshood.

Hukuncin kotu kan ƴancin sanya hijabi?

Alƙalin ya ce makarantar a matsayinta na ta gwamnati, ya kamata ta ba ɗalibai mata musulmi damar ƴancin sanya hijabi.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sheke 'yan ta'adda 7, sun kwato makamai masu yawa a Kaduna

"Makarantar, malamanta, ko wakilanta ba su da hurumin hukunta ɗalibai saboda yin amfani da hijabi a harabar makarantar ko kuma wajen harabar makarantar."

- Mai shari'a, Moshood Abiola

An hana ɗalibai sanya hijabi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin ƙasar Faransa ta haramta ɗalibai sanya ɗalibai musulmai sanya hijabi a makarantun gwmanatin na ƙasar.

Gabriel Attal, ministan ilmi na ƙasar Faransa ya bayyana hijabi a matsayin wata alamar addini ce wacce take kawo barazana ga tsarin kafa makarantu kan yiwa kowane addini adalci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel