Latest
Kungiyar 'yan kasuwan Kano sun shawarci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya mutunta umarnin babbar kotun tarayya wanda ya hana shi nada sabon Sarkin Kano.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shirya korar wasu daga cikin ministocinsa. Shugaban kasar zai sallami ministocin da ba su yin abin kirki a ofis.
Gwamnatin jihar Kano ta musanta jita-jitar da ake yadawa cewa ta samu takardar umarnin kotu kan tube sarakuna biyar da Gwamna Abba Kabir ya yi a jihar.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya soki matakin gwamnatin tarayya na tura sojoji kan rikicin masarautar Kano tsakanin Sanusi II da Aminu Ado.
An shiga jimami bayan sanar da rasuwar tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Lamorde wanda ya rasu a kasar Masar yayin da yake jinya yana da shekaru 61.
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya gana da shugabannin tsaro a jihar kan rikicin masarautar da ke faruwa. Ya gaya musu cewa yanzu gwamnati ta yi masa adalci.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya yi barazanar maka gwamnatin Kano a kotu kan bata masa suna da ta yi a rikicin sarautar jihar.
Gamayyar malaman addinin Musulunci da ke jihar Kano sun yabawa jami'an tsaro da kuma ɓangaren shari'a wurin tabbatar da zaman lafiya a rikicin sarautar jihar.
Osita Chidoka ya soki gwamnatin Najeriya a kan maido alaka da kamfanin Emirates. Ministan jirage ya hada jigon PDP da Atiku ya yi masu kifa daya kwala a dandalin X.
Masu zafi
Samu kari