Abin da Sanusi II Ya Gayawa Shugabannin Tsaro Yayin Ganawarsu a Kano

Abin da Sanusi II Ya Gayawa Shugabannin Tsaro Yayin Ganawarsu a Kano

  • Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya gana da shugabannin tsaro a jihar tare da Gwamna AɓɓaKabir Yusif a fadar Sarkin Kano
  • Sanus II ya gayawa shugabannin tsaron cewa dawo da shi kan sarauta gyara wani zalunci ne da aka yi masa a baya na sauke shi daga sarautar Kano
  • Mai martaba Sarkin ya bayyana musu cewa bai ga umarnin kotu ba wanda ya hana a naɗa shi kan sarautar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Bayanai kan zaman da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi da shugabannin tsaro a jihar Kano sun fito.

A jiya Asabar ne dai gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, Sanusi II da shugabannin tsaron suka gana a fadar Sarkin Kano.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: Atiku ya yi magana kan rikicin sarautar Kano, ya fadi mai laifi

Sanusi II ya gana da shugabannin tsaro a Kano
Sanusi ya gayawa shugabannin tsaro cewa yanzu gwamnati ta yi masa adalci Hoto: @KyusufAbba
Asali: Twitter

Shugabannin tsaron sun kuma yi irin wannan ganawar da Alhaji Aminu Ado Bayero a gidan Sarki da ke Nasarawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Sanusi II ya gayawa shugabannin tsaro?

A cewar wani majiya wanda yake a wajen taron Sanusi II da shugabannin tsaron, Gwamna Abba ya bari shugabannin tsaron sun gana da Sanusi II shi kaɗai, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar ya bayyana cewa shugabannin tsaron sun sanarwa da Sanusi II matakin da suka ɗauka na tabbatar da dokar da ta hana dawo da shi kan sarauta.

Majiyar ya bayyana cewa:

"Sarkin wanda ya yi magana ta tsawon fiye da sa'a ɗaya a lokacin taron, ya gaya mana cewa abin da gwamnatin jihar ta yi adalci ne kan zaluncin da aka yi masa a baya."
"Ya gaya mana cewa bai ga umarnin kotu ba wanda muke magana a kai, inda ya bayyana shi a matsayin kotun yaɗa labarai har sai ya gani da idonsa."

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya sanya labule da Sanusi II, shugabannin tsaro a Kano, bayanai sun fito

Bayan ya karɓi takardar sake naɗa shi kan sarauta daga Gwamna Abba a gidan gwamnatin jihar a ranar Juma'a, Sanusi II ya bayyana cewa dawowarsa ta nuna babu wanda ya isa ya sauya abin da Allah ya ƙaddara zai faru.

Maganar malamai kan sarautar Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar malaman jihar Kano ta yi martani kan abin da ke faruwa a jihar kan matsalar sarautar da ke faruwa.

Malaman sun bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya dauki matakan da suka dace domin kawo karshen matsalar ba tare ta jawo tashin hankali ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel