Malaman Musulunci Sun Magantu Kan Rawar Jami'an Tsaro da Shari'a a Rikicin Sarautar Kano

Malaman Musulunci Sun Magantu Kan Rawar Jami'an Tsaro da Shari'a a Rikicin Sarautar Kano

  • Gamayyar malaman addinin Musulunci da ke jihar Kano sun yi martani kan rawar jami'an tsaro da bangaren shari'a a jihar
  • Malaman sun yabawa jami'an tsaro da kuma ɓangaren shari'a kan tabbatar da zaman lafiya a jihar game da rikicin sarauta
  • Sun kuma yabawa Shugaba Bola Tinubu kan kokarinsa na tabbatar da an bi doka tare da samar da zaman lafiya a jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Malamin Musulunci a jihar Kano sun yi martani kan rawar jami'an tsaro da bangaren shari'a a jihar.

Malaman sun yabawa bangarorin biyu kan rawar da suka taka wajen kawo zaman lafiya da dakile tashin hankali.

Kara karanta wannan

Malaman Musulunci sun tsoma baki a rikicin sarautar Kano, sun gargadi Tinubu

Malaman Musulunci sun magantu kan rikicin sarautar Kano
Malaman Musulunci yabawa jami'an tsaro da bangaren shari'a a Kano. Hoto: Kyusufabba, @iamMacAfeez.
Asali: Facebook

Sanarwar malaman Musulunci a Kano

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da suka sanyawa hannu a jiya Asabar 25 ga watan Mayu, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin malaman akwai Khalifa Sheikh Lawi Atiku Sanka da Khalifa Abdulkadir Ramadan da Farfesa Abdullahi Pakistan da Mallam Yusuf Ahmad Gabari, Pulse ta tattaro.

Sauran sun hada da Mallam Lawan Abubakar Triumph da Sheikh Mohd Bakari da Imam Usaini Yakubu Rano da Imam Jamilu Abubakar da Farfesa Ibrahim Muazzam Maibushira.

Kano: Malaman Musulunci sun yabawa jami'an tsaro

Malaman sun yabawa bangaren shari'a wajen yin hukunci dangane da rusa masarautun da aka yi da mayar da Muhammadu Sanusi II kan kujerar mulki.

"A madadin malamin jihar Kano, muna yabawa dukkan jami'an tsaro da bangaren shari'a a kokarinsu na tabbatar da zaman lafiya a jihar da kuma tsayawa kan doka da yi mata biyayya domin zaman lafiya ya tabbata a jihar Kano."

Kara karanta wannan

Kano: Lamura sun dagule bayan matasa dauke da makamai sun cika fadar Sarki, bayanai sun fito

"Muna kira da gwamnatin jihar Kano da majalisa da su yi taka tsan-tsan wurin ɗaukar matakai da za su kawo matsala a jihar wanda a yanzu haka ma ake cikin matsaloli saboda daukar matakai da ba su dace ba."

- Gamayyar malamai

Har ila yau, malaman sun godewa Shugaba Bola Tinubu kan irin dogewa da ya yi wurin bin doka tare da tabbatar da an samu zaman lafiya a jihar.

Malamai sun gargadi Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar malaman Kano sun ba Bola Tinubu shawara kan yadda za a kaucewa rikici a jihar.

Malaman daga bisani sun bukaci shugaban ya bar ƴan jihar su magance matsalarsu da kansu ba tare da amfani da karfi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.