Kano: Ribadu Ya Ɗauki Zafi Inda Ya Yi Barazana Ga Aminu Gwarzo, Ya Gindaya Sharuda

Kano: Ribadu Ya Ɗauki Zafi Inda Ya Yi Barazana Ga Aminu Gwarzo, Ya Gindaya Sharuda

  • Mallam Nuhu Ribadu ya yi martani mai zafi kan zarginsa da gwamnatin jihar Kano ta yi kan rikicin sarautar jihar
  • Ribadu ya yi barazanar maka mataimakin gwamnan jihar, Abdussalam Aminu Gwarzo a kotu kan kalaman batanci da ya yi a kansa da zarge-zarge
  • Hakan ya biyo bayan zargin Ribadu da hannu a kokarin dawo da Aminu Ado karfi da yaji kan karagar mulkin Kano

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya yi barazanar maka gwamnatin Kano a kotu.

Ribadu ya yi barazanar bayan zarginsa da mataimakin gwamnan jihar Kano ya yi kan dawo da Aminu Ado Bayero garin Kano.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Abba Kabir ya magantu kan sahihancin samun takarda daga kotu

Nuhu Ribadu ya yi barazana ga gwamnatin Kano
Nuhu Ribadu ya bukaci janye kalaman batanci daga mataimakin gwamnan Kano kan kalaman batanci. Hoto: Nuhu Ribadu, Aminu Ado Bayero.
Asali: Facebook

Zargin Ribadu kan rikicin sarautar Kano

Hakan ya biyo bayan martanin Abdussalam Gwarzo inda ya kira sunan Ribadu a matsayin wanda ya ba Aminu Ado jirage biyu zuwa Kano domin mayar da shi karagar mulki, cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata takarda, lauyoyin Ribadu sun bukaci neman afuwa daga mataimakin gwamnan jihar kan wadannan kalamai da ya yi na ɓatanci.

Ribadu zai dauki mummunan mataki kan Gwarzo

"Mun gano wani faifan bidiyo da ke yawo inda mataimakin gwamnan Kano ke zargin Nuhu Ribadu ƙarara a fadar mai martaba sarkin Kano a ranar Asabar 25 ga watan Mayu."
"Kana zargin Ribadu da neman kisan mutanen Kano da kuma lalata dukiyoyinsu a cikin harshen Hausa."
"Dukkan wannan zarge-zarge karya ne kuma nema kake ka batawa Ribadu suna da ofishinsa duk da darajar da ya ke da shi a cikin al'umma."

Kara karanta wannan

Ribadu yana kokarin dawo da Aminu Ado karfi da yaji kan karaga? an gano gaskiya

"Ribadu ya dauki wannan zargi da muhimmanci kuma ya bukaci abubawa biyu daga gare ka cikin awanni 24:
i. Ka janye kalamanka kamar yadda ka yi a gaban mutane da kafofin sadarwa."
ii. Ka nemi afuwa a gidajen jaridu guda biyar da kuma sananniyar kafar gidan jarida ta yanar gizo, sabanin haka Ribadu zai iya daukar matakin shari'a."

- Lauyoyin Ribadu

Ribadu ya musanta hannu a rikicin Kano

Kun ji cewa Mallam Nuhu Ribadu ya musanta hannu a zarginsa da ake yi kan rikicin sarautar jihar Kano.

Ribadu ya ce abin da ake yadawa an yi ne domin bata masa suna kawai a cikin al'umma da kuma jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.