Hajjin 2024: An Shiga Jimami Bayan Rasuwar Maniyyaciya Daga Arewa a Saudiyya

Hajjin 2024: An Shiga Jimami Bayan Rasuwar Maniyyaciya Daga Arewa a Saudiyya

  • An shiga jimami bayan rasuwar daya daga cikin mahajjata a birnin Makka da ke kasar Saudiyya a ranar Asabar 25 ga watan Mayu
  • Marigayiyar wanda ya rasu a jiya Asabar ya fito ne daga jihar Kebbi da ke Arewacin Najeriya bayan ya yi jinya na lokaci kaɗan
  • Mahajjatan jihar Kebbi sune diban farko zuwa kasar Saudiyya a fadin Najeriya wanda aka fara jigilarsu a ranar 15 ga watan Mayu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Makkah, Saudiyya - Hukumar alhazai a Najeriya ta sanar da mutuwar wata maniyyaciya daga jihar Kebbi.

Marigayiyar mai suna Tawalkatu Busare Alako ta rasu ne a ranar Asabar 25 ga watan Mayu bayan ta yi fama da ƴar gajeruwar jinya.

Kara karanta wannan

Hajj 2024: Bayan mutuwar Tawakaltu, wani Alhajin Najeriya ya mutu yana ibada a Saudiya

Maniyyaci daga Kebbi ya kwanta dama a Saudiyya
Hukumar NAHCON ta sanar da rasuwar maniyyaci daga jihar Kebbi. Hoto: Nasir Idris.
Asali: Facebook

NAHCON ta fitar da sanarwa a Saudiyya

Kwadinetan ofishin alhazai da ke Makkah, Aliyu Tanko shi ya sanar da haka a sakon ta'aziyya a madadin shugaban hukumar NAHCON, Jalal Arabi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tanko ya mika sakon ta'aziyya ga hukumar alhazai ta jihar Kebbi inda ya yi addu'ar Allah ya jikansa, cewar TheCable.

Tawagar hukumar alhazai ta kai ziyara bangaren jin dadin alhazai na jihar Kebbi da ke Makkah karkashin jagorancin Garba Takware, Premium Times ta tattaro.

Takware ta godewa tawagar da ziyarar da suka kawo inda ya yi addu'ar gudanar da aikin hajji lafiya a bana.

Daga bisani sun yi addu'ar samun rahama ga mamaciyar da kuma sauran mahajjata da yan Najeriya.

Kebbi: Jihar da aka fara jigilar mahajjata

Alhazan jihar Kebbi sune tashin farko a fadin Najeriya wanda aka fara jigilarsu a ranar 15 ga watan Mayu na wannan shekara da muke ciki.

Kara karanta wannan

"Babu mai daƙile mani hanyar abinci", Shugaban karamar hukuma ya gargadi gwamna

A yanzu haka, an yi jigilar maniyyata 20,154 zuwa Saudiyya yayin da ake tsammanin mutane 65,000 ne zasu gabatar da aikin hajji a bana.

Tsohon shugaban EFCC ya rasu

Kin ji cewa tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Lamorde ya riga mu gidan gaskiya a kasar Masar bayan fama da jinya.

Lamorde ya rasu ne bayan an yi masa tiyata kwanaki uku da suka gabata a kasar bayan yaje neman lafiya a kwanakin nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel