Cashman: Shugaban 'Yan Fim Ya Rasu, Ali Nuhu da Sauran Jarumai Sun Yi Jimami

Cashman: Shugaban 'Yan Fim Ya Rasu, Ali Nuhu da Sauran Jarumai Sun Yi Jimami

  • An tabbatar da rasuwar Umar Maikudi (Cashman), jarumi a shirin Labarina, a ranar Laraba bayan sallar Magriba a birnin Zariya na jihar Kaduna
  • Marigayin ya kasance Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Fina-finai ta Ƙasa kafin rasuwarsa, kuma yana taka rawar lauya a cikin shirin Labarina
  • Fitattun jarumai irinsu Ali Nuhu da Abba El-Mustapha sun bayyana alhini da ta’aziyya, yayin da mabiyansa suka yi masa addu’a a kafafen sada zumunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Masana'antar Kannywood ta shiga jimami da baƙin ciki bayan rasuwar fitattaccen jarumi, Umar Maikudi wanda aka fi sani da Cashman.

Umar Maikudi ya kasance yana taka muhimmiyar rawa a cikin shirin Labarina mai dogon zango da aka dade ana gudanarwa.

Cashman
An sanar da rasuwar jarumin Kannywood, Cahsman. Hoto: Abba El-Mustapha
Asali: Facebook

Ahmad Nagudu ya wallafa a Facebook cewa marigayin ya rasu ne da yammacin Laraba, 21 ga watan Mayu, bayan sallar Magriba a gidan sa da ke cikin garin Zariya, Jihar Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cashman ya kasance shugaban hadaddiyar ƙungiyar masu shirya fina-finai ta ƙasa kafin rasuwarsa, kuma ya bar gagarumin tarihi ga masana’antar shirya fina-finai.

Za a yi jana'izar Cashman a Zariya

Bayanai sun nuna cewa za a gudanar da jana’izar marigayin da safiyar Alhamis a gidansa da ke Zariya.

A madadin daukacin jaruman shirin Labarina da ma’aikata, an mika saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayin da dukkan ƴan uwa da abokan arziki.

Sanarwar da jami'in yada labaran shirin Labarina ya fitar ta ce:

“Allah ya ji ƙan sa, ya sa aljanna ce makoma,”

Rasuwar Cashman ta haifar da jimami a tsakanin masoya da mabiya shirin Labarina da ke kallon rawar da yake takawa a matsayin lauya a cikin shirin.

Ali Nuhu, Abba El-Mustapha sun yi jimami

Daya daga cikin jaruman Kannywood da suka fara nuna ta’aziyya kan rasuwar Cashman shi ne Ali Nuhu, wanda ya bayyana cewa lallai an yi babban rashi.

Ali Nuhu ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa Cashman ya kasance dattijo mai kwazo da kishin ci gaban masana’antar.

Ali Nuhu
'Yan fim sun yi jimamin rasuwar Cashman. Hoto: Ali Nuhu Muhammad
Asali: Facebook

Shi ma jarumi Abba El-Mustapha ya bayyana cewa rasuwar Cashman babban gibi ce da ba za a cike ba cikin sauki.

Masu kallon fim sun yi addu’a wa Cashman

Bayan da labarin rasuwar ya karaɗe kafafen sada zumunta, daruruwan masoya da mabiyan shirin Labarina sun rika rubuta saƙonnin addu’a da jimami.

Wannan rashi ya sake jaddada gagarumar rawar da jaruman fina-finai ke takawa a rayuwar yau da kullum, da kuma yadda al’umma ke jin rashin su a zukatansu.

An dakatar da Labarina da wasu fina finai 21

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar tace fina finai ta jihar Kano ta dakatar da sanya wasu fina finai a fadin jihar.

Rahotanni sun nuna cewa daga cikin fina finan da aka aka dakatar akwai shirin Labarina mai dogon zango da wasu karin 21.

Lamarin ya fara jawo hayaniya a tsakanin masu shirya fina finai da masu kallo, inda aka fara kira ga hukumar ta janye dakatarwar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng