Ana yi wa ‘yan Kannywood shaidar kin zaman aure alhalin kaddara ce ke fito da su – Maryam Malika

Ana yi wa ‘yan Kannywood shaidar kin zaman aure alhalin kaddara ce ke fito da su – Maryam Malika

  • Jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Maryam Malika ta yi martani a kan yadda mutane ke yi wa jarumai mata shaidar kin zaman aure
  • Malika ta bayyana cewa ranta ya kan baci idan ta ga yadda mutane ke mantawa da kaddara wajen shafa masu wannan bakin fenti
  • A cewar ta, burin 'ya mace shine ganinta a dakin mijinta sai dai idan kaddara ta gifta

Shahararriyar jarumar nan ta masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Maryam Muhammad wacce ake yiwa inkiya da Maryam Malika ta yi martani a kan yadda mutane ke yi wa jarumai mata shaidar kin zaman aure.

A wata hira da aka yi da jarumar a shirin ‘Daga bakin mai ita’ wanda sashen Hausa na BBC ke gudanarwa, ta jadadda cewa burin kowace yarinya da iyayenta shine ganinta a dakin aurenta.

Read also

Labarin gimbiyar da ta bar masarautarsu ta auri talaka ya dauki hankalin jama'a

Ana yi wa ‘yan Kannywood shaidar kin zaman aure alhalin kaddara ceke fito da su – Maryam Malika
Maryam Malika ta ce ana yi wa ‘yan Kannywood shaidar kin zaman aure alhalin kaddara ceke fito da su Hoto: BBC
Source: UGC

Malika wacce ta bayyana rashin jin dadinta a kan wannan bakin fenti da ake shafa masu, ta kuma bayyana cewa kaddara ce ke rabo su da dakin mijinsu wanda mutane kan manta hakan.

Ta ce:

“Duk burin wata ’ya mace ita da iyayenta bai wuce ta samu miji ta yi aure ba.
“A lokacin da nake harkar fim Allah Ya kawo min miji na yi aure, muka je na zauna sai ga kuma kaddara wadda ta riga fata, shi ne ya ba ni damar da na sake dawowa harkar fim.
“Yanzu ba ni da wani buri wanda ya wuce Allah Ya fito min da miji na yi aure.
“Gaskiya ba na jin dadi kuma raina yana baci sosai saboda suna nuna kamar cewa ba su san kaddara ba.

Read also

Hoton tsohon rasit da ke nuna an siya buhu 40 na siminti kan N1520 ya janyo cece-kuce

“Ka san dama mu ’yan fim ana cewa ba ma zaman aure, to ba haka ba ne, duk wadda ka ga ta fito daga gidan mijinta kaddara ce, babu macen da za ta so ta yi aure ta fito.
“Ina so mutane su fahimta su san cewa don Allah su daina yada jita-jita a kan abin da ba su gani ba kuma ba su tabbatar ba, idan hakan ta faru ba ma bukatar komai idan ba addu’a ba.”

Adam A. Zango min kishi ne na ki yarda in aureshi, Ummi Rahab

A wani labarin, 'Yar wasar kwaikwayo na masana'antar Kannywood, Ummi Rahab, ta yi magana kan dambarwar da ke tsakaninta da dan wasa kuma mawaki, Adam A. Zango.

A hirar da tayi da DailyTrust, Ummi Rahab ta bayyana cewa Adam A Zange ya cire ta daga wasu fina-funai da ya kamata ace ta fito.

Read also

Yadda kotu ta daure wani mutum shekaru 10 kan satar da abokinsa ya tafka

Amma a ra'ayinta, wannan ba komai bane saboda a matsayinsa na ubangidanta, yana da ikon cireta daga Fim.

Source: Legit.ng News

Online view pixel