An Yi Rashi a Kannywood: Yaya Ɗanƙwambo na Shirin Gidan Badamasi Ya Rasa Mahaifiyarsa
- Allah ya karbi rayuwar mahaifiyar Nura Yakubu, wanda aka fi sani da Yaya Ɗanƙwambo, a ranar Lahadi, 19 ga Janairu 2024
- Shugaban shirin Gidan Badamasi, Falalu A. Dorayi ya sanar da rasuwar, yana mai yin addu’ar Allah SWT ya gafarta mata
- A hannu daya, mahaifin jarumin barkwanci, Baba Ari ta rasu, kuma an yi mata sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Allah ya karbi rayuwar mahaifiyar jarumin barkwanci, Nura Yakubu wanda aka fi sani da Yaya Ɗanƙwambo a shirin Gidan Badamasi.
An rahoto cewa mahaifiyar Yaya Ɗanƙwambo ta rasu ne a ranar Lahadi, 19 ga watan Janairun 2025 kuma an yi mata sutura kamar yadda addini ya tanadar.

Asali: Instagram
Kannywood: Mahaifiyar Yaya Ɗanƙwambo ta rasu
Shugaban shirin Gidan Badamasi, Falalu A. Dorayi ne ya sanar da rasuwar mahaifiyar Yaya Ɗanƙwambo a shafinsa na Instagram.

Kara karanta wannan
'Dan Majalisar Tarayya na Kano na tsaka mai wuya, yunƙurin tsige shi ya kara tsananta
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daraktan fina finan ya ce tuni aka yiwa mamaciyar jana'aiza a layin Hayin Dogo da ke garin Samarun Zaria, jihar Kaduna.
Falalu A. Dorayi ya yi Addu'ar Allah ya jikan mahaifiyar Yaya Ɗanƙwambo, ya kuma kyautata ta su mutuwar idan ta zo.
Sanarwar da Falalu A. Dorayi ya fitar
Falalu A. Dorayi ya wallafa cewa:
"InnalilLahi Wa'inna ILaihi Raji'un.
"Allah ya yi wa mahaifiyar Nura Yaya Dankwambo rasuwa @nura_dankwambo
"An yi janaizarta a Samarun Zaria, Hayin Dogo.
"Allah ya yi mata gafara, ya bai wa iyalai da 'yan uwa hakurin rashinta, idan mutuwarmu ta zo ,Allah ka sa mu cika da imani, Amin."
Kannywood: Mahaifin Baba Ari ya rasu
A wani labarin makamancin wannan, Allah ya karbi rayuwar mahaifin dan wasan barkwanci, Aminu Baba Ali, wanda aka fi sani da jarumi Baba Ari.
Shugaban hukumar tace fina finai da dab'i ta jihar Kano, kuma jarumin Kannywood, Abba El-Mustapha ya sanar da rasuwar a shafinsa na Instagram.
Abba El-Mustapha ya sanar da cewa:
"InnalilLahi Wa'inna ILaihi Raji'un.
"Allah ya yiwa mahaifin jarumi Aminu Baba Ari rasuwa kuma an yi jana'izarsa kamar yadda adinin Musulunci ya tanadar."
Shugaban hukumar tace fina finan ya yi addu'a ga mamacin yana mai cewa:
"Muna addu’ar Allah ya jikansa, ya gafarta masa kurakuransa, ya sa Aljanna madaukakiya ce makomarsa. Idan ta mu ta zo kuma Allah ya sa mu cika da kyau da imani."
Kakar 'yar wasar Kannywood ta rasu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, iftacciyar 'yar wasar Kannywood, Rahama Sadau, ta rasa kakarta da take matukar kauna, abin da ya jefa ta cikin alhini.
Hajiya Rahama Sadau ta bayyana tsananin kaduwarta, tana mai yabawa gata da soyayyar da kakarta ta nuna masu a lokacin da take raye.
Tuni dai jarumai, abokan sana'a, da masoyanta suka rika taya ta alhini game da wannan babban rashi da ta fuskanta a farkon shekarar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng