Bayan Dogon Jira, An Sanya Ranar Fara Haska Fim din 'Gidan Badamasi' Zango na 6
- Kamfanin Dorayi Films ya sanar da dawowar shirin Gidan Badamasi zango na shida bayan gama zango na biyar a karshen 2022
- Masu kallon wannan shirin sun kasance cikin tsumayin ganin zango na shida tun a 2023, amma ba su dace ba sai a shekarar nan
- Falalu Dorayi ya bayyana cewa zango na shida zai kawo sababbin salo na barkwanci, yayin da ya saki wasu jerin tallace-tallace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - A Disambar 2022, kamfanin Dorayi Films ya sanar da fitar shirin Gidan Badamasi zango na biyar, kashi na 13, wanda ya zama kashin karshe a zangon.
Tun da shekarar 2023 ta shiga, masu kallo ke ta tsumayin ganin zango na shida na shirin, amma babu labari har sai a watan Disambar 2024 da muke ciki.
Gidan talabijin din Arewa24 ya yi sanarwa a shafinsa na Facebook, cewa zango na shida na shirin Gidan Badamasi zai dawo a tsakiyar Disamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gidan Badamasi zango na 6 na nan tafe
A cewar sanarwar:
"Albishirin ku. Shirin Gidan Badamasi Zango na shida yana nan tafe a ranar 19 ga watan Disamba da misalin karfe 6:00 na yamma."
Sai dai kuma, gidan talabijin din ya nuna cewa shirin zai rika zuwa ne a kan manhajarsa ta Arewaondemand, ba tare da fadin ko za a rika haskawa a talabijin ba.
A mafi yawan lokuta, Arewa24 ba ta haska fina finan da take dorasu kacokan a kan manhajarta, misali shi ne shirin 'Wata Rana a Kano' na Abubakar Bashir Maishadda.
Kadan daga shirin Gidan Badamasi zango na 6
Mai shirya shirin Gidan Badamasi, Falau A. Dorayi ya wallafa wasu gajerun tallace tallace a shafinsa na Instagram da ta yi tsokaci kan shirin zango na shida.
A talla ta farko, an ga Tijjani Asase (Adamahama) da jaruma Hadiza Kabara (Hauwa) a cikin kayan gidan yarin, yayin da Falau ya wallafa cewa:
"Adahama da Hauwa an yi abin kunya, an tafi gidan yari."
A wata tallar kuma, an ga Yaya Dan Kwambo a cikin mota yana yiwa su Bazuka tsiya tare da barazanar daure su, yayin da Falalu ya yi bayani cewa:
"Wannan gudu ne tsakanin kare da zomo, wane ya saci kudi, wane na neman ya za ayi ya karbi kudinsa."
Jarumi kuma mai ba da umarni, Falalu A Dorayi ya nuni da cewa Gidan Badamasi zango na shida zai zo da abubuwan salo na barkwanci da ba a gani a baya ba.
Gidan Badamasi ya fito da jaruma Azeema
A wani labarin, mun ruwaito cewa jarumar Kannywood, Hauwa Ayawa ta sanar da cewa shirin Gidan Badamasi ne ya fito da tauraruwarta har ta yi haske.
Hauwa da a yanzu aka fi sani da Azeema Gidan Badamasi ta taka rawar 'yar Alhaji Badamasi a shirin, kuma ta nuna kwarewa a matsayin da aka ba ta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng