An Shiga Jimami a Kannywood yayin da Jaruma Rahama Sadau Ta Yi babban Rashi

An Shiga Jimami a Kannywood yayin da Jaruma Rahama Sadau Ta Yi babban Rashi

  • Jarumar fina finan Hausa, Rahama Sadau, ta sanar da rasuwar kakarta wadda ta ce ta taka rawa daga yarinta zuwa girmasu
  • A ranar Alhamis, ta wallafa a shafukan sada zumunta cewa mutuwa ta ziyarce su, kuma sun rasa wani bangare na rayuwarsu
  • Tuni dai jarumai, abokan sana'a da kuma masoyan Rahama Sadau suka rika tururuwar taya ta alhinin wannan babban rashi da ta yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta yi babban rashi yayin da kakarta ta rigamu gidan gaskiya.

Rahama Sadau ta nuna tsananin kaduwarta da rasuwar kakarta, wadda ta ce ta nuna masu gata da soyayya a lokacin da take raye.

Allah ya yiwa kakar Rahama Sadau rasuwa
Rahama Sadau ta sanar da rasuwar Kakakarta a ranar Alhamis. Hoto: Rahama Sadau
Asali: Facebook

Kakar Rahama Sadau ta rasu

A cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram a ranar 28 ga Nuwamba, Rahama Sadau ta ce:

Kara karanta wannan

Badakalar N80.2bn: Kotu ta yi fatali da bukatar EFCC a shari'ar tsohon gwamnan Kogi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A yau mutuwa ta ziyarce mu kuma mun rasa wani bangare na rayuwarmu. Kakarmu wadda ta taka rawa a rayuwarmu ta rigamu gidan gaskiya.
"Muna rokon Allah ya jikanta da Rahama, ya sanya ta a gidan Aljannah Firdausi."

Jarumar ta kara da cewa:

"Allah ya jikanki Hajiya. Allah ya yi miki rahama, ya sa Aljannah ce makoma a gareki. Ameen.
"InnalilLahi wa inna iLaihir rajiun."

Kalli sanarwar a nan kasa:

'Yan Kannywood sun yi wa Rahma Sadau ta'aziyya

falalu_a_dorayi ya yi magana, yake cewa:

"Allah ya jikanta ya ba ku hakurin rashinta."

salisufulani10

"Allah ya gafarta mata Ameen."

salisufulani10

"Allah ya mata rahama. Muna ta'aziyya."

'Yar wasar nan real_maryamyahaya ta ce:

"Allah ya mata rahama."

official_hairat11

"Allah ya gafarta mata, ya yi mata rahama."

madam__korede

"Allah ya sa ta huta."

Ita kuwa officialmaryambooth ta rubuta:

"Allah ya mata rahama."

Sai nafeesat_official ta ce:

"Allah ya yi mata rahama."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Tsohuwar Minista Ta Sake Komawa Kotu Bayan Tinubu Ya Kore Ta

Tinubu ya ba Rahama Sadau mukami

A wani labarin, mun ruwaito cewa Rahama Sadau ta samu kujera a kwamitin shirin saka hannun jari a fannin kirkire-kirkiren zamani (iDICE).

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima wanda ya kaddamar da shirin domin tallafawa masana'antar kirkire-kirkire ya sanar da 'yan kwamitin.

A yayin kaddamar da shirin, Shettima ya ce majalisar zartarwa ta amince a fitar da $617.7m domin gudanar da shirin a jihohi 36 da Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.