Sadiq Saleh, Ado Gwanja da Wasu Mawakan Kannywood 5 da Suka Yi Tashe a 2024

Sadiq Saleh, Ado Gwanja da Wasu Mawakan Kannywood 5 da Suka Yi Tashe a 2024

  • Mawakan da suka yi tashe a 2024 sun hada da sababbi da tsofaffi, wakokinsu sun yi tashe a gidajen biki da soshiyal midiya
  • Sadiq Saleh shi ne mawaki mafi shahara a shekarar 2024 yayin da wakokinsa irin su Mai Kishina da Kallon Soyayya suka yi tashe
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wasu mutane kan mawakan da suka fi so, inda suka bayyana bamnbancin Umar da sauran mawaka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ba shakka shekarar 2024 ta zama abar tunkaho ga mawakan Hausa da dama, musamman wadanda suka fito daga masana'antar Kannywood.

Daga Janairu zuwa Disamba, an ga bullar sababbin mawaka, kamar irinsu Sadiq Saleh da tauraruwarsu ta haska har ta zarce ta wasu tsofaffin mawakan.

Mawakan Kannywood 5 da suka shahara a 2024
Sadiq Saleh, Ado Gwanja da wasu mawakan Kannywood 3 da suka shahara a 2024. Hoto: adogwanja, sadiqsalehofficial, umarmshareef
Asali: Instagram

Legit Hausa ta yi nazarin mawakan da suka yi tashe a shekarar 2024 ta hanyar la'akari da wakokin da suka fitar, tasirin wakokin a shafukan sada zumunta da sauransu.

Kara karanta wannan

An farmaki wata maboyar gaggan barayi a Kano, an kwato kayan da suka sace

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da sababbin mawaka suka nuna bajintarsu, haka su ma dadaddun mawakan irinsu Ado Gwanja, Umar M Shareef sun nuna cewa "mai zamani ya kiyayi mai laya."

Ga jerin mawaka 10 da suka yi tashe a 2024:

1. Sadi Saleh - 'Mai Kishina'

Sadiq Saleh shi ne mawakin Kannywood mafi shahara a 2024 wanda wakokinsa suka ja hankalin jama'a, musamman a gidajen biki.

A shekarar 2024, ya fitar da wakoki da suka yi tashe kamar: 'Mai Kishina, Ko Wuya Ko Dadi, Kallon Soyayya, Dadin Soyayyya da sai sauransu,

Wadannan wakoki sun nuna kwarewarsa wajen hada kalamai masu jan hankali da sauti mai dadi, wanda ya sa 'yan mata ke bin wakokin a TikTok da sauran kafafen sada zumunta.

2. Ado Gwanja

Ado Gwanja ba bako ba ne a duniyar wakokin Hausa, domin kuwa an yi lokacin da wakokinsa suka karade ilahirin garuruwa da kasashen da ke jin Hausa.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Sojoji sun kashe hatsabibin shugaban ƴan bindiga da yaransa a Katsina

Wakokin Ado Isa Gwanja sun yi bamban da na sauran mawaka, kuma farin jininsa ya fi karfi a wajen mata. Zai yi wuya a hada taron mata ba a kunna wakar Gwanja ba.

A shekarar 2024, Ado Gwanja ya fitar da wakoki da suka yi tashe kamar irin su: Na Fada Soyayya, Bani, Ragass da Hajiya Tambara.

Ado Gwanja yana da saukin shiga zukatan matasa. Wakokinsa suna da farin jini a wajen bukukuwa, wanda ya sa ya kwashe dogon lokaci ana damawa da shi.

3. Umar M Shareef

Umar M Shareef mawaki ne da ke tafiya da salo, wanda ya sa kowace shekara ya ke shiga jerin mawakan da suka yi tashe a wannan shekarar.

Wakokin Umar M Shareef da suka yi tashe a 2024 sun hada da: 'Na Ji Na Ga ni, Tawa, Inda Rabbana, Ruwan Ido, So Sanadi da sauransu.

Har yanzu kundin karshe na 'Lokaci Ya Yi' da Umar M Shareef ya fitar na ci gaba da zama abin sauraro ga masoyan wakokin Hausa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dakile mummunan harin 'yan bindiga, sun ceto mutane da dama

Baya ga wakoki, Umar M Shareef shi ma jarumi ne a masana'antar Kannywood.

4. Auta Waziri

Auta Waziri ya kasance matashin mawakin Hausa wanda ya yi fice wajen wakokin soyayya. A shekarar 2024, ya fitar da wakokin da suka yi tashe sosai.

Wakokin Auta Waziri da suka kara masa farin jini a 2024 sun hada da: Aljannata, Zuciya, Sarauniya, Na Baki So da dai sauransu.

Mawaki Auta Waziri yana amfani da salon zamani da kuma gargajiya wajen tsara wakokinsa. Wannan ya sa ya ci gaba da samun karbuwa sosai a masana'antar nishadantarwa ta Arewa.

5. Auta MG Boy

Auta MG Boy fitaccen mawakin Hausa ne da ya yi fice a cikin 'yan shekarun nan, musamman a shekarar 2024.

Ya shahara da wakokinsa masu ratsa zuciya da kuma salon kidan zamani wanda ke jan hankalin matasa da ma manya.

A cikin 2024, ya fitar da wakoki da dama da suka samu karbuwa sosai, ciki har da 'Nagode, Ummme da Ba Damuwa."

Kara karanta wannan

El Rufai, Shetty da mutane 17 da Tinubu ya ba mukamai amma daga baya ya soke nadin

Wadannan wakoki sun nuna kwarewarsa wajen hada kalmomi masu ma'ana da kuma sauti mai kayatarwa, wanda ya kara masa farin jini a tsakanin masoya.

Karin wasu mawakan mawaka 10:

6. Nazifi Asnanic

7. Hamisu Breaker

8. Abdul D One

9. Salim Smart

10. Kawu Dan Sarki

11. Nura M Inuwa

12. Ali Jita

13. Namenj

14. Umar MB

15. DJ AB

"Bambancin Umar da sauran mawaka"

A zantawar Legit Hausa da wasu matasa a jihar Kaduna, an samu ra'ayoyi da suka nuna bambancin mawaki Umar M Shareef da sauran mawaka.

Abba Officer ya ce:

"Takani ga Allah na fi son wakar Umar M Shareef saboda wakarsa ta masoya ce, kuma ni kaina ina soyayya. Idan ina jin wakokinsa ni ma ina samun kalaman da nake yiwa masoyiya ta."

Abubakar Sadiq ya ce:

"Shi Umar M Shareef ya fi su iya wakar soyayya da murya mai taushi, shi ya sa nake sonsa."

Kara karanta wannan

Neman aiki, rabon abinci da sauran lokutan da 'yan Najeriya suka mutu a wajen turmutsutsi

Mallam Abbas kuwa ya ce duk mawakan Hausa babu wanda yake so sama da Nura M Inuwa, yana mai cewa:

"Ni gaskiya Nura M Inuwa ya fi burge ni, saboda idan kana sauraron wakokinsa za ka fahimci inda ya dosa, da sakon da ya ke son isarwa."

Abdullahi Nice B ya ce:

"Ni na fi son wakar Umar, ina da wakokinsa kala kala. Mawaki ne wanda bai taba wulakanta ni ba kuma dan Rigasa ne, sannan wakarsa ta fi mun."

Ado Gwamnja ya saki sabon kundi

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen mawakin Hausa, Ado Gwanja ya saki sabon kundi mai dauke da wakoki 18 da ya yiwa take da 'Dama Ni ne.'

Mawakin ya saki kundin ne a ranar 20 ga watan Disambar 2024, kuma yana dauke da wakokin da suka hada da Cikina, Duniya Labari, Dama Ni ne da sauransu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.