Dandalin Kannywood: Abubuwa 5 da baku sani ba game da Ado Gwanja
- Abubuwa 5 da baku sani ba game da Ado Gwanja
- Shin dan asalin jihar Kano ne
- Mahaifiyar sa ba bahausa bace
- Yana yin wakokin fina-finai, siyasa da kuma biki
Kusan a iya cewa dukkan masu sha'awar harkokin fina-finan Hausa musamman ma mata sun san fitaccen mawakin nan watau Ado Gwanja.
Shi dai Ado Gwanja a baya an fi ganin sa ne a cikin fina-finai a matsayin dan daudu amma kwatsam sai tauraruwar sa ta soma haskawa a fagen wakoki musamman ma na biki.
Jarumin kuma fitaccen mawaki dai yana da matukar farin jini a tsakanin 'yan mata da ma matan aure domin irin salon kidan sa da yake yi.
Yanzu dai a iya cewa matashin yana daga cikin wadanda tauraruwar su ke haskawa a farfaciyar masana'antar nishadantarwa a Kannywood.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Auren wata jarumar fim din Hausa ya mutu kasa da wata 3 da daurawa
Ga dai wasu daga cikin muhimman abubuwan da watakila baku sani ba game da jarumin, kuma mawaki:
1. Ana yi masa lakani da Limamin mata
2. Shi ruwa biyu ne, ma'ana; mahaifin sa bahaushe ne dan asalin Kano ne, mahaifiyar sa kuma Shuwa Arab ce 'yar asalin garin Maiduguri.
3. Waka ya fara kafin shiga harkar fim domin kuwa ya shafe shekaru akalla 12 yana yin waka amma ba'a san shi ba.
4. Yana da uban gida a harkar wata. Aminu Mai Dawayya shine uban gidan sa.
5. Yana yin wakar siyasa idan ya samu ba na biki kawai yake yi ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng